Ƴan bindiga sun kashe sojoji biyu da wasu mutane uku a jihar Nasarawa

Ƴan bindiga sun kashe sojoji biyu da kuma wasu mutane uku a yayin da suka ƙona gidaje da dama a Umaisha dake ƙaramar hukumar Toto ta jihar Nasarawa.

Ba wannan ne karon farko ba da ƴan bindiga su ke kai wa jami’an tsaro hari ba a yankin ko da a ranar 7 ga watan Faburairu ƴan bindigar sun kashe sojoji uku da fararen hula biyu a wani harin kwanton ɓauna da suka kai musu a ƙauyen Katakpa dake maƙota da Umaisha.

Har ila yau a ranar 25 ga watan Faburairu ƴan bindigar sun kai farmaki ƙauyen na Katakpa suka kashe baraken gargajiya na garin, Abubakar Ahmadu tare da wasu mutane 11 da kuma ƴan sanda biyu tare da ƙona gidaje ciki har da marigayin.

Da yake tabbatar da harin na baya-bayan nan wani mazaunin Katakpa, Ibrahim Sa’idu ya ce lamarin ya faru ne 02:33 na daren ranar Laraba lokacin da ƴan bindiga suka ƙaddamar da farmaki kan ƙauyen Shege.

“Abin da ya faru sojojin da aka ajiye a Katakpa sun ƙarbi kiran kai ɗaukin gaggawa a yayin da suke kan hanyarsu ne ƴan bindigar su kai musu kwanton ɓauna inda suka kashe sojoji biyu nan take,” ya ce.

Ya ce an kai gawarwakin sojojin babban asibitin Toto inda daga nan aka kai su Cibiyar Kula Da Lafiya ta Tarayya dake Lafiya.

More from this stream

Recomended