Wasu ‘yan bindiga sun sake kai hari da sanyin safiyar ranar Alhamis a kauyen Kuka Babangida da ke karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina, inda suka kashe mutane akalla tara ciki har da hakimin kauyen, Idris Haruna.
Shugaban karamar hukumar Bashir Sabiu ya tabbatar da faruwar lamarin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Katsina, ASP Abubakar Aliyu, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin.
Rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyen ne ‘yan mintuna kadan kafin tsakar dare inda suka yi ta kai farmaki har zuwa karfe 1:30 na safiyar ranar Alhamis.
Mazauna kauyen sun ce ‘yan fashin sun dauki lokaci suna bi gida-gida suna neman wasu abubuwa masu daraja da suka hada da kudi.
Hat yanzu dai tsuguno bai ƙare ba a Arewacin Najeriya inda har yanzu ake samu tashe-tashen hankula da suka hada da satar mutane da kashe-kashe.