Zuckerberg ya ce yanzu mutane za su iya amfani da WhatsApp ɗinsu a kan wayoyi har huɗu

Mark Zuckerberg, mamallakin Facebook, ya bayar da sanarwar cewa masu amfani da WhatsApp daga ranar Talata za su iya amfani da akawun ɗinsu na WhatsApp a kan wayoyi har guda huɗu a lokaci guda.

Zuckerberg dai ya bayyana hakan ne a ranar Talata cikin wata sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kafin yanzu, masu amfani da WhatsApp ɗin za su iya shiga WhatsApp ɗin nasu ne ta waya ɗaya kawai.

Sama da mutane biliyan 2.24 ne ke amfani da WhatsApp kowane wata, wanda hakan ya sa ya zama ɗaya daga cikin shahararrun manhajojin wayar hannu na duniya.

More News

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani ɓangare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...

Matatar Mai Ta Kaduna Za Ta Fara Aiki A Ƙarshen 2024

Kamfanin Kaduna Refining and Petrochemical Company KPRC ya ce matatar mansa za ta fara aiki a shekarar 2024. Mustapha Sugungun managan matatar man ta KRPC...

Manyan dillalan mai za su fitar da litar man fetur miliyan 300 a wannan makon

Ƙungiyar MEMAN ta manyan dillalan man fetur da dangoginsa ta ce mambobinta sun fara lodin mai har lita miliyan 300 a cikin makon nan...

Kotu ta ɗaure mutumin sa ya yi sama-da-faɗi da kuɗin marayu

Babbar kotu a jihar Borno ta yanke wa Isiyaku Ibrahim hukuncin shekara ɗaya a gidan yari da zaɓin biyan tarar naira dubu 100 saboda...