Zaben 2019: kalmomin da suka shafi zabe wadanda ya kamata ku san su

A


Accreditation
(Tantance masu zabe)
:
Wannan tsari ne da ake bi kafin a fara zabe domin tantance wadanda suka cancanta su jefa kuri’a.

B


Ballot Box
(Akwatin Zabe)
:
Wani nau’in akwati ne rufaffe wanda ake jefa kuri’a a cikinsa.

Ballot Paper
(Takaradar Zabe)
:
Takarda ce wadda ke dauke da sunayen yan takara.

Bye-election
(Zaben cike gurbi)
:
Wani nau’in zabe ne da ake gudanarwa domin cike gurbin wani mai rike da mukamin siyasa bayan ya mutu. Zai iya yiwuwa kuma idan mai rike da mukamin ba zai iya ci gaba da zama kan kujerar ba sakamakon kiranye da aka yi masa ko kuma wani kalubale da aka samu na soke zaben, misali a sakamakon magudi.

C


Card Reader
(Na’urar tantance masu zabe)
:
Wannan na’ura ce da ke tantance katin zabe na dindindin (PVC) domin a tabbatar mallakin wanda ke dauke da shi ne.

Claim
(Korafi)
:
Korafi dai wata hanya ce da ake bi a lokacin lika sunayen masu zabe domin sanar da hukumar zabe sunayen da ba a saka ba a rajistar ko ba a rubuta su daidai ba domin a gyara.

D


Display
(Likawa)
:
Wannan shi ne yadda ake lika takardar rajistar masu zabe a bainar jama’a domin dubawa, idan akwai kura-kurai sai a gyara.

E


EMB
:
Sashen gudanar da zabe. (Wannan shi ne sashen da ke gudanar da zabe). Akwai sassan gudanar da zabuka 37 a Najeriya. Akwai Hukamar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da kuma hukumomin zabe masu zaman kansu na jihohi (SIEC) guda 36.

Election Observers
(Masu sa ido a zabe)
:
Masu sa ido a zabe mutane ne da suka hada da kungiyoyin da hukumar zabe ta amince da su domin duba yadda zabe ke gudana (raba kayan zabe da tantance wa da kirga kuri’u da tattara alkaluman zabe da kuma bayyana sakamako). Akwai masu duba zabe iri biyu. Akwai na cikin gida kana akwai na kasashen waje.

Election monitors
(Masu duba zabe)
:
Masu duba zabe jami’ai ne da hukamar zabe ta ke turawa rumfunan zabe domin duba yadda ake gudanar da zabuka.

G


General Elections
(Babban zabe)
:
Babban zabe shi ne zaben da ake yinsa a kasa baki daya wanda ya fara tun daga karamar hukuma har matakin tarayya, ana yin sa ne bayan kayadadden lokaci domin zaben wakilan da zasu wakilci jama’a bayan karshen wa’adin wadanda suke kan mulki.

I


INEC
:
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Ta Kasa

Inconclusive election
(Zaben da bai kammalu ba)
:
Wannan zabe ne da ake yi idan aka samu cewa yawan kuri’un da aka soke ko kuma yawan wuraren da ba a yi zabe ba za su iya shafar sahihancin sakamakon zaben a mazabar da aka gudanar da shi.

M


Manifesto
(Manufofi)
:
Manufofi a harkar zabe wata takarda ce wadda ta ke kunshe da kudurorin jam’iyya a kan yadda za ta gudanar da mulki idan taci zabe. Manufofin na bayani a kan taken jam’iyya da kuma irin burin da take da shi na kawo cigaba ga al’umma.

N


Nomination
(Gabatar da dan takara)
:
Gabatar da dan takara yana daga cikin hanyoyin da jam’iyyu suke bi domin zaben dan takarar da ke neman wata kujera

O


Objection
(Kin amincewa)
:
Nuna kin amincewa wata hanya ce ta gabatar da koke ga hukumar zabe a kan cewa akwai sunan wanda bai cancanta ya jefa kuri’a ba a takardar rajistar masu zabe.

Open secret ballot system
(Dangwala kuri’a a sirrance)
:
Wannan wani tsari ne wanda mai jefa kuri’a ke dangwala kuri’arsa cikin sirri kafin ya saka ta cikin akwatin zabe a bainar jama’a.

Opposition
(Jam’iyyar adawa)
:
Wannan ita ce babbar jam’iyya wadda tafi magoya baya amma ba ta da gwamnati.

P


PRV
(Takardar rajistar masu zabe)
:
Wannan wata rajista ce wadda ke dauke da sunaye da kuma sauran bayanai na wadanda aka yi wa rajistar zabe. Ana wallafa takardar rajistar masu zabe ne a bainar jama’a domin masu zaben su duba sunayensu, idan akwai kura-kurai, korafi ko kuma sunayen da ba a fitar da su ba sai a sanar domin a gyara.

PVC
:
Katin zabe na din-din-din.

Party Agent
(Wakilin Jam’iyya)
:
Wakilin jam’iyya mutum ne wanda ke wakiltar jam’iyya ko kuma dan takara a rumfar zabe ko kuma wurin tattara sakamakon zabe a ranar zabe.

Party primary
(Zaben Fidda gwani)
:
Zaben fidda gwani, zabe ne da jam’iyya take zaben wanda zai tsaya takara karkashin inuwarta a lokacin zabe.

Polling unit
(Rumfar Zabe)
:
Rumfar zabe wani wuri ne da hukumar zabe ta amince domin a jefa kuri’a.

R


Re-run election
(Maimata zabe)
:
Wannan zabe ne da ake yi ida an tafka magudi ko kuma ba a bi ka’idojin zabe ba a karon farko.

Recall
(Kiranye)
:
Kiranye wata hanya ce wadda masu zabe suke bi domin tsige mai wakiltar su tun daga matakin kansila, har zuwa matakin majalisa.

Rejected ballot
(LalataCciyar kuri’a)
:
Lalatacciyar kuri’a ana samun ta ne idan ra’ayin mai jefa kuri’a bai bayyana ba yadda ya kamata a kan takardar zabe. Misali, Idan inda aka dangwala bai hau kan gurbi sosai ba, ma’ana ya tsaya tsakanin guraben ‘yan takara biyu ko kuma ba a dangwala takardar zaben yadda ya kamata ba. irin wannan kuri’ar, ba za a kirga ta ba a matsayin kuri’a ga kowane dan takara.

Return
(Sakamako)
:
Wannan ana nufin shelar da jami’in zabe ke yi na ayyana dan takarar da ya lashe zabe ne a karkashin dokar zabe ta kasa

Returning Officer (RO)
(Baturen Zabe)
:
Baturen zabe jami’in hukumar zabe ne wanda yake da alhakin bayyana sakamakon zabe a ranar zabe.

Run-off election
(Zabe zagaye na biyu)
:
Ana yin wannan zaben ne lokacin da zaben da aka yi a karon farko ba samar da wanda ya lashe zaben ba a matakin gwamna ko shugaban kasa. Wannan na faruwa ne idan dan takarar da yafi yawan kuri’u bai samu adadin kuri’un da doka ke bukatar ya samu ba a fadin jiha ko a kasa baki daya.

S


SIEC
:
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Ta Jiha (Dukkan jihohi na da irin wannan hukumar da ke gudanar da zabukan kananan hukumomi).

T


Tactile Ballot Paper
(Takardar jefa kuri’a ta masu nakasa)
:
Takardar jefa kuri’a ce ta musamman wadda ta ke bada dama ga makafi ko matsalar ido domin jefa kuria’r su cikin sirri ba tare da an taimaka masu ba

Tendered ballot paper
(Kuri’ar da wani yayi amfani da ita)
:
Wannan takardar kuri’a ce da ake mika wa mai son kada kuri’a wanda wani ya hau kan damarsa ta jefa kuri’a. Bayan an yi mata alama, sai a mika ta ga jami’in zabe mai kula da wannan rumfar zaben, amma ba za a saka ta cikin akwatin kada kuri’a ba.

Turnout
(Yawan mutanen da suka fito jefa kuri’a)
:
Wannan shi ne yawa ko kuma wani kaso na mutanen da suka cancanta su jefa kuri’a kuma suka fito rumfar zabe domin jefa kuri’a.

More News

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...

Matatar Mai Ta Kaduna Za Ta Fara Aiki A Ƙarshen 2024

Kamfanin Kaduna Refining and Petrochemical Company KPRC ya ce matatar mansa za ta fara aiki a shekarar 2024. Mustapha Sugungun managan matatar man ta KRPC...

Manyan dillalan mai za su fitar da litar man fetur miliyan 300 a wannan makon

Ƙungiyar MEMAN ta manyan dillalan man fetur da dangoginsa ta ce mambobinta sun fara lodin mai har lita miliyan 300 a cikin makon nan...

Kotu ta É—aure mutumin sa ya yi sama-da-faÉ—i da kuÉ—in marayu

Babbar kotu a jihar Borno ta yanke wa Isiyaku Ibrahim hukuncin shekara ɗaya a gidan yari da zaɓin biyan tarar naira dubu 100 saboda...