Za Mu Shiga Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani A Yau Juma’a, Cewar Ma’aikatan Jami’a – AREWA News


Gamayyar Kungiyoyin Ma’aikatan Jami’o’in Nijeriya sun kammala washin wukarsu ta shiga yajin aikin sai baba ta gani a yau Juma’a, 5 ga watan Fabrairun 2021.
Kungiyoyin da suka hada da na manyan ma’aikata SSANU da kuma ma’aikata marasa koyarwa a jami’oin kasar NASU sun yanke hukuncin haka ne sakamakon watsi da bukatunsu da gwamnatin tarayya ta yi.
A yayin zantawarsa da Aminiya ta hanyar wayar tarho, Shugaban SSANU Muhammad Haruna Ibrahim, ya ce sun yanke shawarar tsunduma yajin aikin a yayin wani taro na cimma matsaya da suka gudanar a tsakanin shugabancin kungiyoyin biyu a ranar Alhamis.
Mista Haruna ya ce an aike da wasikar umartar dukkanin ’ya’yan kungiyoyin da su bayar da hadin kai domin tabbatar da an gurgunta harkokin ilimi a jami’o’in kasar daga ranar Juma’a.
Ya jaddada cewa gwamnatin tarayya ta gaza tabbatar da jarjejeniyar da suka kulla bayan wa’adin kwanaki 14 da suka bata domin ta waiwayi bukatunsu.
Shugaban na SSANU ya ce yajin aikin na sai baba ta gani zai fara ne daga karfe 12 na daren ranar Juma’a matukar ba a samu sauyin kudiri ba a tsakanin rassanta da ke fadin kasar.
Idan ba a manta ba a watan jiya na Janairu ne gamayyar kungiyoyin ma’aikatan suka gudanar zanga-zangar lumana domin yi wa gwamnatin tarayya matsin lambar warware bukatunsu da suka hada tsarin raba Naira biliyan 40 na alawus-alwawus a tsakanin ’ya’yanta da na kungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU.
Sauran bukatun da matsalolin da kungiyoyin ke bukatar ganin an shawo kansu sun hada da takaddamar da ta dabaibaye sabon Tsarin Biyan Albashi na bai daya (IPPIS), inda da dama ake zaftare wani kaso na albashinsu da ake biya ta wannan tsari.

More News

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani ɓangare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...

Matatar Mai Ta Kaduna Za Ta Fara Aiki A Ƙarshen 2024

Kamfanin Kaduna Refining and Petrochemical Company KPRC ya ce matatar mansa za ta fara aiki a shekarar 2024. Mustapha Sugungun managan matatar man ta KRPC...

Manyan dillalan mai za su fitar da litar man fetur miliyan 300 a wannan makon

Ƙungiyar MEMAN ta manyan dillalan man fetur da dangoginsa ta ce mambobinta sun fara lodin mai har lita miliyan 300 a cikin makon nan...

Kotu ta ɗaure mutumin sa ya yi sama-da-faɗi da kuɗin marayu

Babbar kotu a jihar Borno ta yanke wa Isiyaku Ibrahim hukuncin shekara ɗaya a gidan yari da zaɓin biyan tarar naira dubu 100 saboda...