Ministan aiyuka, David Umahi ya ce za a dauki karin watanni 24 kafin a kammala aikin titin Abuja zuwa Kano.
Umahi ya bayyana haka ne a ranar Juma’a lokacin da ya kai ziyarar duba aikin tare da ministan kuɗi, Wale Edun.
A ranar 5 ga watan Janairu ne ministan ya ce gwamnatin tarayya za ta kammala aikin a karshen shekarar 2024.
Umahi ya bayyana cewa kawo yanzu an kammala aikin titin daga Kaduna zuwa Zariya a yayin da ya rage sauran kilomita 20 a kammala aikin a tsakanin Kano zuwa Zaria.
Ana sa bangaren ministan kuɗin, Wale Edun ya tabbatarwa da ministan cewa samar da kudin yin aikin ba zai zamo matsala saboda yadda gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ta mayar da hankali kan samar da abubuwan more rayuwa.
A shekarar 2018 ne gwamnatin shugaban kasa, Muhamed Buhari ta bayar da aikin bisa cewa za a kammala shi a watanni 36.