Connect with us

Hausa

Za a kafa sabuwar gwamnati a Sudan ta kudu | BBC Hausa

Published

on

Shugaban Sudan ta Kudu ta Salva Kiir
Image caption

Gamayyar kungiyoyin farar hula a Sudan ta Kudu, sun yi kira ga kwamitin tsaro na MDD ya yi kokarin kafa sharuddai da dokokin da za su kare kasar daga sake fadawa yaki.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da kungiyoyin suka fitar bayan saba lokacin da aka cimma yarjejeniyar zaman lafiya da ya kamata a ce ta fara aiki a ranar 12 ga wannan watan.

Kungiyoyin rajin kare hakkin jama’a 200 ne suka tattaunawa da fitar da abubuwa guda 5 da suke fatan ganin kwamitin tsaro na MDD ya yi dan sake gina sabuwar sudan ta kudu wadda yakin basasa na shekara 5 ya daidaita.

Geoffrey Duke shi ne jagoran wannan tafiya, ya kuma ce abu na farko su na bukatar sabon kwamitin wanzar da zaman lafiya tsakanin bangarortin da ke rikici da juna da kuma suka rattaba hannu kan yarjejeniyar su yi kokarin samar da gwamnatin hadaka daga nan zuwa 12 ga watan Nuwamba mai zuwa.

Sannan kwamitin tsaro na MDD ya sauke hakkin da ya rataya akan sa na kare farar hular Sudan ta Kudu, da kuma daukar irin matakin da aka dauka a baya.

Sai kuma kasashe makofta su tabbatar ba a shiga ko fota da makamai daga kasar zuwa cikinsu ba, da tabbatzr da ba a sace ma’adinai da dukiyar kasa ta hanyar tsallaka iyakokinsu ba.

Haka kuma kungiyar tarayyar afirka ta samar da kotun hukunta manyan laifuka a Sudan ta Kudun, kamar yadda aka gabatar da bykatar hakan a lokacin tattunawar sulhu.

A karshe masu zuba jari na kasashen waje su dawo kasar dan farfado da wannan bangaren ba wai zuba jari kadai ba har da ba da gudummawar farfado da dimukradiyyar kasar. Inda za su zuba ido kan shugabannin kasar yadda da sun karya wata doka daga cikin dokokin da aka shardanta za a hukuntasu.

A watan Satumbar bara ne dai aka yi zaman sulhunta shugaba Salva Kiir da tsohon mataimakinsa kuma madugun ‘yan tawaye Riek Machar da ya ke gudun hijira bisa radin kan sa, amma daga wancan lokaci zuwa yanzu ba bu wani abun azo a gani da aka cimma da nufin ci gaban Sudan ta kudun.

Mr Duke, ya ce wadanda alhakin komai ya rataya a kansu su na da watanni 6 nan gaba da za su yi aiki tare dan kawo karshen halin da ‘yan Sudan ta Kudun suke ciki.

Facebook Comments
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Kudin bai-daya na iya durkusar da tattalin arzikin Najeriya

Published

on

—BBC Hausa

Bayan amincewa da yarjejeniyar kudi na bai’daya da kasuwanci maras shinge a Afirka, masana na ganin tattalin arzikin Najeriya bai yi karfin da zai mamaye na sauran kasashen nahiyar ba.

A kwanan baya ne Najeriya da sauran kasashen Afrika ta Yamma karkashin kungiyar ECOWAS, suka yanke shawarar fara amfani da takardar kudi ta bai-daya ta ECO, zuwa badi .

Haka kuma Najeriyar ta yanke shawarar shiga cikin yarjejeniyar kasuwanci maras shinge da sauran kasashen Afrika.

Wasu na ganin kasancewar Najeriya a yarjejeniyar yana da matukar amfani, saboda matsayin tattalin arzikinta a Afirka, kamar yadda kuma wasu ke ganin amincewa da yarjejeniyar zai bunkasa kasuwanci da samar da dubban ayyukan yi.

Sai dai duk da ana yi wa Najeriya kallon mafi karfin tattalin arziki a tsakanin kasashen nahiyar, masana na ganin hakan ba zai sa ta iya mamaye kasuwancin sauran kasashen ba.

A hirarsa da Ahmad Abba Abdullahi a shirin Gane mini Hanya, Dr Dauda Muhamad Kwantagora, wani masanin tattalin arziki a Najeriya ya ce tattalin arzikin kasar ya dogara ne da fetir maimakon tattalin arziki na kere-kere da bunkasar sha’anin noma ba.

Ya ce kasashen duniya ne ke tsayar da farashin fetir wanda tattalin arzikin Najeriya ya dogara da shi, kuma farashin yana hawa ne yana sauka.

“Tana iya mamaya idan tana da girman masana’antu na kere-kere da arzikin samar da abinci da za su iya gogayya da shan gaban na sauran kasashen Afirka,” in ji shi.

Masanin ya kuma ce idan har Najeriya tana son more yarjejeniyar, sai ta bi tsari kamar irin yadda Birtaniya ta yi a yarjejeniyar Tarayyar Turai inda ta rike kudinta maimakon amfani da kudin bai-daya na yuro.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Najeriya na dogaro ne da arzikin Fetir

Ga dorewar tsarin, masanin na ganin dole sai ya kasance an gudanar da mafi yawancin kasuwancin tsakanin kasashen na Afirka.

Wannan shi ne babban kalubalen da za a iya fuskanta, domin yawancin kasashen Afirka sun fi hulda ne da kasashen waje maimakon makwabtansu na nahiyar.

Kasuwanci tsakanin kasashen Afirka bai wuce kashi 16 ba duka. A tsakaninsu da kasashen yankin Asiya kuma kashi 51, a Turai kuma adadin ya kai kashi 70.

Hakan ya nuna yana da wahala kasuwancin na bai-daya ya karbu cikin lokaci kankani.

Facebook Comments
Continue Reading

Hausa

Amsar tambayoyinku kan Hamadar Sahara | BBC Hausa

Published

on

sahara

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Wannan makala ce da ta amsa tambayoyin da masu sauraro suka aiko kan Hamadar Sahara. Mun yi bincike tare da jin ta bakin masana kan yankin da kuma wasu mutane da suka taba keta wannan hamada mai matukar girma.

Gabatarwa

Hamadar Sahara ita ce waje na uku mafi girma a duniya da mutane ba sa rayuwa a cikinsa, baya ga Antarctica da kuma Arctic. Sai dai ita Sahara ita ce waje mafi tsananin zafi a ban kasa, yayin da Antarctica da kuma Arctic kuwa suka kasance masu tsananin sanyi.

Girmanta ya kai nisan kilomita miliyan 9.4, kusan kashi daya bisa na uku na girman nahiyar Afirka, wato kenan kusan girman kasar Amurka da ta hada da Alaska da Hawaii.

Sahara ta dauki kusan kashi 30 cikin dari na dukkanin kasashen da ke Afirka. Kuma Sahara tana tsakiya ne a Afirka, kuma wuri ne da ke samun karancin ruwa.

BBC Hausa ta yi nazari ta hanyar tattaunawa da Masana ilimin yanayin kasa da kuma wadanda suka taba rayuwa da kuma ratsa Sahara, wadanda kuma suka yi kokarin amsa wasu tambayoyi da kuka aiko mana.

Hamadar SaharaBBC
Muhimman bayanai kan Sahara

Yanki mafi tsananin zafi a duniya

  • Shekarun samuwartaMiliyan 100
  • Yawan kasashen da Sahara ta ratsa11
  • Girmanta a kilomitaMiliyan 9.4
  • Ma’aunin zafi na celsius47-50

Bayani: Farfesa Maharazu Yusuf Bebeji BUK

Asalin SaharaTambayar da mafi yawan masu sauraro suka aiko kenan amma ba su bayyana sunayensu ba

Asalin sunan Sahara ya samo asali ne daga harshen Larabci wato Sahra. Sahara ta kunshi mafi yawancin yankin arewacin Afirka da ke kan iyaka da yankin Sahel da kuma kasashen kudu da Sahara.

Kasashen Sahara sun hada da Aljeriya da Chadi da Masar da Libiya da Mali da Sudan da Tunisiya da Murtaniya da Nijar da kuma kasar Yammacin Sahara.

Wani masanin yanayin kasa Farfesa Maharazu Yusuf Bebeji na Jami’ar Bayero, Kano, ya ce bincike ya nuna cewa a da can shekaru aru-aru wannan yankin ba Hamada ba ce.

Ya ce wasu masu bincike sun samu wasu abubuwa da suke nuna cewa da can ita Sahara wuri ne da ke da damshi da koguna, amma samuwar yawaitar mutane a Afirka ne ya sa ruwa ya janye a wajen.

“Masana sun ce wannan ya faru ne fiye da shekara miliyan 100,” in ji shi.

Ya ce masu bincike sun ce an samu kwale-kwale a sahara sannan an hako manya-manyan halittu kamar Dinasours da aka tsinto a Sahara, wanda ke nuna a can shekaru miliyoyin da suka wuce babu Sahara.

Farfesa Maharazu ya ce “Kuma Dinasour ba ya rayuwa sai wuri mai dausayi, kuma an same shi ne a yankin Agadez.”

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Yawanci gine-ginen kasa ne a yankunan daji na Sahara

Shin asalin Sahara, teku ce ta kafe?

Masanin ya ce Sahara ba teku ba ce ta kafe, domin sahara da muke da ita tana da tudu, kuma ya fi girman Najeriya wanda ke nuna cewa ba teku ba ne.

Akwai wani bangare wanda ya yi kasa da ake zaton cewa an samu tafkuna kamar Tafkin Chadi da ake tunanin sun ajiye ruwa.

Sai dai ya ce faruwarta, shi ne wurin da ke samun karancin ruwa.

“Wuri ne da iska ke tashi, ba a samun ruwan sama, sai gefenta ne ake samun sau daya tak a shekara. Wani lokaci a wata daya tak.”

Amma masanin ya ce akwai lokacin da take da dausayi, kuma kamar yadda inda ba Sahara ba yake da dausayi akwai kuma lokacin da yanayin yake komawa na Sahara.

Shin tun asali akwai Sahara

Farfesan ya ce da can akwai Sahara, shekaru aru-aru tun kafin zuwan mutane.

“Shi dan adam ba a dade da samunsa ba a duniya” in ji masanin.

Ya ce kamar wasu garuruwan arewacin Najeriya, a shekaru aru-aru can baya Sahara ne.

Bincike ya nuna cewa daga baya ne yankin ya samu daga Sahara kamar yadda ake gurgusar da teku.

Hamadar SaharaBBC
Kasashen da Sahara ta ratsa sosai

A kasashen nahiyar Afirka

  • 30%Girman yankin da Sahara ta mamaye
  • 95%Yawan Hamadar da ke Masar
  • 60%Yawan Hamadar da ke Aljeriya
  • 60%Yawan Hamadar da ke Nijar

Bayani: Farfesa Maharazu Yusuf Bebeji BUK

Shin Hamadar Sahara da kasashe nawa ta hada iyaka? Sannan yankin wacce kasa ne ya fi yawa?

Wadannan tambayoyi ne da muka samu daga dumbin mutane wadanda ba su bayyana sunayensu ba.

Ilimin yanayin kasa ya nuna cewa yankin Sahara ya yi iyaka da Tekun Atlantika daga yamma, da Kogin Maliya daga gabas, da Bahar Rum daga arewa sannan daga kudu ta yi iyaka da yankunan da ke da ciyayi amma ba bishiyoyi da yawa wato Sahel Sabana.

Wannan kasurgumin waje ya ratsa kasashe 11 na Afirka da suka hada da Aljeriya da Chadi da Masar da Libiya da Mali da Mauritaniya da Moroko da Nijar da Yammacin Sahara da Sudan da kuma Tunisiya.

Kuma daga cikinsu an bayyana cewa, kasar Masar ce ta fi yawan Sahara. Wato ita ce ta fi yawan girman Hamadar Sahara.

“Kashi 95 na Masar kusan Hamada ce, sai Aljeriya da kuma Nijar, wacce kashi 60 cikin 100 na kasar hamada ce.” in ji Farfesa Maharazu.

Wadanne irin halittu da kuma tsirrai ke iya rayuwa a Hamada?

Wannan ma wata tambaya ce daga masu sauraro kusan shida.

Masana sun ce akwai halittu da ake gani a Hamada, wadanda ake ganin Allah Ya ba su kariya da za su iya rayuwa ba tare da ruwa ba.

Halittun suna da abin da za su iya ajiye ruwa, irinsu Gawo da Kafto wadanda za su iya zama tsawon lokaci ba tare da sun damu da ruwa ba.

A bangaren tsirrai akwai Dabino da ke da saiwa mai zurfi, ana samunsa ne a Hamada.

A bangaren dabbobi, akwai Rakumi wanda ake kira “Jirgin Hamada” da kan dauki kwanaki kamar mako daya ko kwana 10 ba tare da ya sha ruwa ba.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ana yawan ganin rakumi wanda ake kira “Jirgin Hamada” da kan dauki kwanaki kamar mako daya ko kwana 10 ba tare da ya sha ruwa ba

Akwai kadangaru, da suke juriyar wahala, da za su iya daukar lokaci ba su nemi ruwa ba. Masana sun ce dangin kadangare da macizai za su iya jure wa karancin ruwa a hamada.

Farfesa Maharazu ya ce duk da cewa akwai wurare masu zurfi da za a iya samun ruwa a Sahara, amma halittun suna da wata halitta da Ubangiji ke kare su da zafin rana na Hamada.

Ya ce kamar yadda ake samun halittun ruwa, haka akwai halittun da ba za su iya rayuwa ba sai a wannan yanayi na Sahara. “Haka Allah Ya yi su.”

Wani mutum dan kasar Nijar Abu Ila, da ya taba ratsa Sahara don zuwa Libiya ya ce ya ga tsuntsaye nau’i uku, amma bai ga tsirrai ko bishiyoyi ko gini ba.

Yanayin Sahara

Hamada tana da nau’i biyu, tana da karancin ruwa da kuma zafi. Farfesa Maharazu ya ce a lokacin rana, zafi a Sahara yakan kai ma’aunin celcius 47 zuwa 50.

Da dare kuma yanayin zai koma na sanyi, inda ma’aunin zai sauka ya dawo zuwa 15.

Ya ce halittun duk da ke rayuwa, Allah zai ba su juriyar zafi da kuma sanyin Hamada.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Dubban ‘yan ci-rani ne ke tafiya Turai daga Afirka inda su kan bi ta Agadez kuma suna tafiyar kwana 40 a Sahara

Samun ruwan sama a Sahara

Abu Ila ya ce a kwanakin da suka yi suna tafiya “an yi ruwan sama jefi-jefi.”

Masana sun kasa Hamadar Sahara kashi biyu – akwai Aric inda ake samun ruwan sama, wadanda za su iya yin noma.

Akwai kuma inda ba a samun ruwa, da ake kira Hypa Aric a Turance, kamar yankin Arlit zuwa Aljeriya, inda ake iya shafe shekara ba a yi ruwa ba.

Farfesa Maharazu ya ce akwai wani wuri a yankin Masar da aka ce an yi shekara sama da 40 ba a yi ruwa ba. Haka kuma ya ce a wuraren kudancin Agadez ana iya shuka saboda sukan samu ruwa.

Sai dai Abu Ila ya ce a tafiyar da ya yi a cikin Sahara bai ga ko da tsiro daya da ke nuna alamar ana iya shuka a wurin ba.”

Abin da ke kawo sanyi da zafi?

Masanin yanayi Farfesa Maharazu ya ce yawancin makamashi da muke samu daga hasken rana ne. Kuma Hamada babu bishiyoyi, sai rairayi kuma a haka rana ta kan zo ta fadi.

Ya ce ba kamar yankin da ba Hamada ba inda itatuwa da bishiyoyi ke rike zafin da rana ta buga, amma a Hamada babu.

Dalilin da ya sa Sahara ke yin sanyi

Farfesa ya ce gajimare ya kan rike zafin da duniya ta dumama da shi daga hasken rana, amma Hamada tun da babu wannan gajemaren, to a bude sama take.

“Idan tururin ya bugi kasa nan da nan sai ya huce ya yi sama sai wuri ya yi sanyi,” in ji shi.

Ana samun ruwan sha a Sahara?Masu sauraro sun aiko da wannan tambayar

Abu Ila ya ce a tafiyar da suka yi cikin Sahara dai da guzurin ruwan shansu suka tafi, kuma rijiya biyu kawai suka gani a cikin Sahara.

“Rijiyoyin kuwa su ne wacce ake cewa metal wacce take a jikin gini kuma ba ruwa a cikinta, sai kuma Ashugur ita kuma akwai ruwa a cikinta,” in ji Abu Ila.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Masana sun ce an hako manya-manyan halittu kamar Dinasours da aka tsinto a Sahara a can baya

Ta yaya Hamada ke kwararowa?

Masu bincke sun tabbatar da cewa lallai Hamada tana gurgusowa, saboda sauyin yanayi. Yawan ruwan da ake samu ya ragu, wanda hakan ke nuna gurgusowar Hamada.

Al’umma ta yawaita, an mayar da wurare wurin noma da kiyo, wanda ke haifar da kwararowarta.

Nijar daya daga cikin kasashen da suka fi fuskantar barazanar kwararorwar Hamada, ta fi daukar matakan kariya.

An bullo da wani tsari na sassaben zamani, inda ake koyawa manoma yadda ake sassabe ba tare da kwalkwale komi ba, sai dai a yi sama-sama domin dakile kwararowar hamada.

Ya zurfin yashin hamada?

Masana sun ce akwai Hamada mai tsakuwa da duwatsu, akwai kuma mai kasa.

Kuma a cewar Farfesa Maharazu, Hamada mai tsakuwa tana da zurfi, amma ya danganta da yawan kasar da iska ta tara.

Ya ce yawanci iska ce take tara kasa a Sahara. Kuma yawanci zurfin yakan kai mita 10 zuwa mita 20.

“Mun yi wani bincike a arewacin Karamar Hukumar Yusufari ta jihar Yoben Najeriya, akwai wadda za ka samu ta kai zurfin mita 50 zuwa 100,” in ji masanin.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

garin Arawan kenan da ke arewacin Timbuktu na Mali kafin Sahara ta gurgusa ta rufe wajen a shekarar 2002

Akwai arzikin da ake samu a Sahara?

Masana sun ce akwai arziki sosai a yankin Hamadar Sahara a Afirka.

Kuma masanan sun ce rashin ruwa ba zai hana samun arziki ba ko da kura da iska sun ruguza ko sun lullube duwatsu tsawon shekaru.

Amma ba zai hana a samu ma’adinai ba, domin an samu man fetir a Nijar da Gas.

Akwai kuma zinari da ake hako wa a yankin Agadez da kuma arzikin Uranium.

Akwai kuma ma’aidanai da yawa a yankin Aljeriya da Nijar da Masar.

Facebook Comments
Continue Reading

Hausa

Damisa ta kwanta baccin rana a kan gadon wani magidanci a Indiya

Published

on

A tiger lying on a bed in Assam state

Damisar ta hau kan gado ta kwanta a cikin wani gida dake jihar Assam

An gano wata macen damisa wacce ta tsere daga wani gandun namun daji a jihar Assam da ambaliyar ruwa ta daidaita a Indiya, kwance a kan gadon wasu mazauna jihar.

Ana tunanin ta gudo ne daga Gandun Namun Daji na Kaziranga inda dabbobi 92 suka mutu a ‘yan kwanakin nan saboda ambaliyar ruwa.

Jami’an wata kungiyar masu fafutukar kare hakkin namun dawa sun isa gidan kuma sun samar wa damisar hanyar fita zuwa daji.

A cewar Gidauniyar Namun Dawa ta Indiya WTI, an fara ganin damisar ne kusa da wani babban titi ranar Alhamis.

Gidauniyar ta ce babu mamaki, kaiwa da komawar da ake yi a kan titin ya matsa mata don haka ta nemi wannan gidan ta shiga, wanda kuma a kusa da babban titin yake.


Mai gidan ya tsere a lokacin da ya tsinkayi damisar

Rathin Barman wanda ya jagoranci cire damisar daga gidan ya ce ta shiga gidan ne da misalin karfe 7 da rabi sannan ta kwanta ta yi ta bacci gaba daya ranar.

“Ta yi matukar gajiya kuma ta samu bacci mai kyau,” a cewarsa.

Sai dai Migidan, Motilal, ya tattara kan iyalinsa kaf a lokacin da ya ga shigowar damisar.

“Abin sha’awa shi ne babu wanda ya matsa mata don ta samu hutawa sosai. Muna matukar girmama namun dawa a wannan yankin,” in ji Mista Barman.

“Molitilal ya ce zai adana zanin gadon da matashin kan da damisar ta hau ta kwanta.”

Jami’an WTI sun tsayar da motoci a kan babban titin tsawon awa guda sannan aka tayar da dabbar daga bacci. Ta tashi sannan ta bar gidan da misalin karfe biyar da rabi na yamma, ta tsallaka titin sannan ta bi hanyar dajin.

Mista Barman ya ce babau tabbacin cewa ta shiga dajin ko kuma da shiga wani wajen ne dake kusa da dajin.

Gandun Namun Daji na Kaziranga na ajiye Damisa 110 amma babu ko daya da ya mutu a ambaliyar ruwan.

Dabbobin da suka mutu a dandun sun hada da barewa 54 da dorinar ruwa 7 da aladen dawa 6 da giwa daya.

Ambaliyar ruwa ta daidaita jihohin gabashin kasar na Bihar da Assam, inda ta kashe sama da mutane 100 da raba miliyoyin mutane da muhallansu.

Lokacin ruwa, wanda ke farawa daga watan Yuni zuwa watan Satumba ya jefa Nepal da Bangladesh cikin rudani.

Facebook Comments
Continue Reading
Advertisement
Advertisement

Trending

%d bloggers like this: