Za a bude ofisoshin gwamnati ranar Litinin a Lagos – AREWA News

Gwamnatin jihar Lagos ta bayar da umarni a bude ofisoshi da sauran hukumomin gwamnati daga ranar Litinin 04 ga watan Mayu.

A wata sanarwa ranar Juma’a, shugaban ma’aikata na jihar, Hakeem Muri-Okunola ya ce gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu ya amince da sake bude ofisoshin gwamnati a matsayin wata hanya ta aiwatar ta janye dokar kulle da aka saka a jihar.

Ya ce ma’aikata dake matakin albashi na 12 zuwa kasa za su cigaba da aiki daga gida a yayin da ake shawartar marasa lafiya da su kauracewa zuwa wurin aiki baki daya.

Ya kara da cewa ba a bawa jama’ar gari ko kuma ma’aikatan da aka hana zuwa aiki damar zuwa ma’aikatun ba.

More from this stream

Recomended