Yawan mutanen da suka mutu daga mummunan ambaliyar ruwan da ta samu birnin Derna dake gabashin kasar Libiya sun haura dubu 11300 a cewar Majalisar Dinkin Duniya(MDD) kamar yadda hukumar agaji ta Red Crescent dake kasar ta fada.
Karin wasu mutane 10100 ne suka bace a birnin.
A wasu wuraren dake gabashin kasar ta Libiya wajen birnin na Derna ambaliyar ta kashe akalla mutane 170.
Sanarwar ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana sa ran yawan mutanen zai cigaba da karuwa a yayin da ake cigaba da nema da kuma ceto jama’a.
Har ila yau ana cigaba da fuskantar karancin ruwan sha inda kawo yanzu yara 50 suka kamu da ciwo daga shan gurbataccen ruwa.