
Labaran da suke fitowa daga wurin taron zaben fitar da gwani na dan takarar shugaban kasa a jam’iyar APC dake gudana yanzu haka a Abuja sun bayyana cewa gwamnonin jam’iyar sun sake rage yawan yan takarar shugaban kasa a jam’iyar ya zuwa uku.
Tuni suka mikawa shugaban kasa, Muhammad Buhari sunan, Rotimi Amaechi, Bola Ahmad Tinubu da kuma mataimakin shugaban kasa,Yemi Osinbajo.
Tun da farko gwamnonin sun rage yawan yan takarar zuwa biyar kafin daga bisani su sake bada shawarar rage su zuwa uku.
Shugaban kasa Muhammad Buhari shi ne ya nemi gwamnonin da su shawo kan sauran yan takara da su hakura su janye takarar su.
Matakin na gwamnonin baya na nufin ragowar yan takarar basu da ikon shigar takara ba.