Yan Sanda Uku Sun Mutu a Hatsarin Mota a Kaduna

Yan sanda uku ne aka rawaito sun mutu a wani hatsarin mota a Kidanda dake karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

LYan sandan na kan hanyarsu ta komawa Giwa ne bayan da suka halarci bikin Hawan Daushe a garin Zariya a ranar Lahadi lokacin da hatsarin ya faru da misalin karfe 09:00 na dare.

Tayar ɗaya daga cikin motocin da suke ciki ce ta fashe a wajen kauyen Sako dake mazabar Kidanda har ta kai ga mutuwar yan sandan.

Uku daga ciki da suka jikkata an garzaya da su asibiti domin samun kulawar likitoci.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kaduna, Muhammad Jalinge ya tabbatar da faruwar hatsarin

More from this stream

Recomended