‘Yan sanda sun tsare mata biyar masu sayar da jirirai

FACEBOOK

Hakkin mallakar hoto
FACEBOOK

Image caption

Madam Ify ita ke jagorantar nemo yaran kuma ta sayar da su kan naira dubu 950

Wasu mata biyar da suke saye da sayar da ƙananan yara sun fada hannun jami’an ‘yan sanda, a daidai lokacin da suke tattauna yadda za su sayi wani yaro a yankin Rumuokwuta da ke Obio Akpor a jihar Rivers da ke Najeriya.

Wani hoton bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta ya nuna wata mata mai suna Roseline Nwokocha da ‘yar uwarta Chioma sun je Port Harcourt daga birnin Umuahia domin sayen wani yaro kan N1,100,000.

A bidiyon, Roseline Nwokocha ta ce ba wannan ne karon farko da ta shiga wannan kasuwanci ba, tana mai cewa sama da mako biyu tana zuwa sayen yaran.

Ta ce sun je sayen wani yaro ne kan kudi sama da miliyan daya ita da kanwarta, Chioma, wacce ta bi ta domin ta ga yadda ake wannan kasuwanci.

Ta yi bayanin cewa abokiyar harkarta mai suna Chichi ce ta kira ta, ta ce za a samu wasu yaran nan da mako biyu shi ya sa suka je saya.

Duka matan biyar da suke wannan mummunan kasuwanci sun fada komar ‘yan sanda.

Chichi ta ce suna sayar wa Roseline yaran kan naira miliyan daya saboda su ma suna samunsu daga wajen mai kawo musu, Madam Ify, kan naira 950,000 idan sun sayar suna samun ribar dubu 50 ne kawai.

Roseline Nwokocha ta ce tana sayar da yaran kan N1,100,000 ga mutanen da suke mayar da su ‘ya’yansu a birnin Umuahia sai ta samu ribar 100,000 kan ko wanne yaro.

Nwokocha ta je Port Harcourt ne da garin kudi N1,100,000 domin ta biya kudin yaron da ta gani daga wajen wata mata, Madam Ify ce ya kamata ta kawo yaran bayan sun kama su.

Madam Ify ta ce an kira ta ana son sayan yaro sai ta nemi Chichi domin binciko wane ne yake son siyan yaron domin bata san kowa nene ba, kuma sun kira ta ne a matsayin ma’aurata da ke son sayen yaran, ta ce ba za ta iya tuna su ba amma ga sunan a wayarta.

Ta biyar din kuwa wata bakar mace ce da ta fito a bidiyon kuma itace mahaifiyar yaron da aka siya mako biyu baya, sai dai ba su ambaci sunanta ba.

Yanzu dai wannan turka-turka na gaban hukumar ‘yan sanda ta jihar Rivers, kuma da zarar an samu karin bayani kan binciken da ake gudanarwa za mu kawo muku.

More News

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye aikinsa na wani lokaci

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya ajiye aikinsa na wani lokaci domin tunkarar matsalar lafiya.Mista Ngelale...

Ali Jita ya koma jam’iyar APC daga NNPP

Mataimakin shugaban majalisar dattawa dattawa, Sanata Barau Jibrin ya karɓi fitaccen mawakin Kannywood, Aliyu Isa Jita daga jam'iyar NNPP ya zuwa jam'iyar APC. Ali Jita...

An yi jana’izar mutumin da ya ƙirƙiri tutar Najeriya

Iyalan marigayi, Pa Taiwo Akinkumi mutumin da ya ƙirƙiro tutar Najeriya sun yi bikin binne shi bayan da gwamnatin tarayya ta gaza cika alƙawarin...

‘Za a ƙara wa ƴan bautar ƙasa na NYSC alawus’

Babban daraktan hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC) Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa ‘yan bautar kasar cewa za a kara...