Yan sanda sun kama yan bindiga biyu sma Kaduna

Rundunar yan sandan jihar Kaduna ta ce jami’anta sun samu nasarar kashe wani dan bindiga guda daya a Rigachukun dake karamar hukumar Chikun tare da kama wasu biyu a yankin Saminaka.

A yayin artabun da aka gwabza da yan bindigar rundunar ta ce wasu daga cikin yan bindigar sun tsere da raunin harbin bindiga.

Sanarwar ta ce an kai samame ne a maboyar yan bindiga inda aka gano bindigar AK-47 guda daya da kuma mashingan ƙirar gida guda ɗaya da harsashi 10.

More from this stream

Recomended