
Rundunar yan sandan jihar Kano ta ce ta kama wani mai suna Abba Musa mazaunnin jihar ɗauke da kwayar Tramadol da darajarta ta kai miliyan ₦25.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa shi ne ya sanar da haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.
A cewar Kiyawa an kama mutumin ranar Lahadi da karfe 10 na dare akan titin Ahmadu Bello Way.
Jami’an yan sanda na caji ofis din Badawa su ne suka kama matashin lokacin da suke gudanar da binciken ababen hawa akan titin karkashin DPOn su Muhammad Yakubu.
Tun da farko Abba wanda yake zaune a unguwar Rijiyar Zaki dake birnin Kano ya ce abokinsa,Sulaiman Danwawu shi ne ya mallaki motar dake ɗauke da kwayar kuma ya bashi ne ya kai ta wurin wani a unguwar Yan Kaba.
Bayan da aka kamo Sulaiman ya tabbatar da cewa shi ne ya mallaki motar kuma ya sayo kwayar ne daga jihar Anambra.