
Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Shell na aikin hakar man fetur da sarrafa iskar gas a yankin Neja Delta
‘Yan sandan sun tabbatar da sace wasu manyan ma’aikatan babban kamfanin hakar man fetur biyu tare da kashe ‘yan sandan da ke tsaronsu a yankin Neja-Delta mai fama da rikici a Najeriya.
Harin ya faru ne lokacin da ma’aikatan ke dawowa daga wata tafiya ranar Alhamis a kan titi cikin jihar Ribas.
‘Yan bindigar sun kashe jami’an tsaro, a cikinsu har da matukin motar, kafin su kama ma’aikatan na kamfanin Shell.
Mai magana da yawun ‘yan sanda na cewa ana kokarin ceto ma’aikatan da aka sace.
Ba a dai bayyana sunaye da kasashen da suka fito ba.
Wani mai magana da yawunsa ya ce: “Kamfanin Aikin Man fetur na Shell a Nijeriya (SPDC) na nadamar tabbatar da harin da aka kai kan ma’aikatansa da kuma jam’an tsaron gwamnati a Rumuji, jihar Ribas, a kan titin East/West”.
Ma’aikatan na dawo ne daga wata tafiya da suka yi zuwa jihar Bayelsa.
Satar mutane don neman fansa, abu ne ruwan dare a Najeriya inda ake hakon turawa ‘yan kasashen waje da ma sauran ‘yan Najeriya, a baya-bayan nan har da mutanen karkara.
A farkon wannan wata ma, Wasu ‘yan bindiga sun kashe wata ‘Yar Burtaniya bayan sun je wani wurin shakatawa a cikin jihar Kaduna. An kuma sace karin mutum uku yayin harin ban da wadanda aka kashe.