Yan sanda sun dakile hari kan ofishin su

0

Rundunar yan sandan jihar Enugu ta ce jami’anta sun samu nasarar dakile wani hari  da bindiga suka suka kai kan ofishin yan sanda na shiya dake karamar hukumar Igbo-Eze North.

Daniel Ndukwe, mai magana da yawun rundunar shi ne ya sanar da haka cikin wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce yan sandan sun dakile  harin ne a ranar 21 ga watan Yuli da karfe 6:00 na yamma.

Ya ce bata gari “sun zo da yawa” inda suka fara harbin kan me uwa da wabi akan ofishin.

Mai magana da yawun rundunar ya ce jam’ansu sun yi musayar wuta da bindigar inda ya kara da cewa babu da jikkata a ciki.

Amma kuma ya ce wasu daga cikin maharan sun samu raunuka sanadiyar musayar wuta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here