Yan sanda sun ceto wasu ƴan mata daga gidan karuwai

Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra sun ceto wasu ‘yan mata biyu da ba su kai shekaru 18 ba, wadanda ake amfani da su wajen karuwanci a wani samame da suka kai wani otel a unguwar Oba, karamar hukumar Idemili ta kudu a jihar.

An yi wannan farmakin ne biyo bayan wani bayani daga wani mai fallasa bayan an ci gaba da gudanar da ayyukan assha a kusa da otal din.

An ce za a kai ‘yan matan asibiti domin a duba lafiyarsu.

Da take jawabi jim kadan bayan kai farmakin a ranar Laraba, kwamishiniyar kula da harkokin mata da jin dadin jama’a ta jihar Ify Obinabo, ta yaba da kokarin jami’an tsaro wajen taimakawa wajen ceto ‘yan matan.

More from this stream

Recomended