
Rundunar yan sandan jihar Nasarawa, ta ce jami’anta sun ceto wani malamin jami’ar jihar Nasarawa.
Malamin mai suna, Isaac Igbawua na fannin nazarin ƙananan kwayoyi halittu anyi garkuwa da shi ne ranar 27 ga watan Disamba.
Ramhan Nansel, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ya ce rundunar ta samu bayanai cewa wasu yan bindiga sun dira gida malamin dake Old Barracks a karamar hukumar Kokona.
Nansel ya ce yan sandan sun kuma samu bayanan sirri da suka taimaka musu wajen bin sahun yan bindiga zuwa wani daji dake Ogba a Nassarawan Eggon.
Ya ce hakan ya kai ga yin musayar wuta da yan bindigar a ranar 28 ga watan Disamba har ta kai ga an kubutar da malamin jami’ar ba tare da kwarzane ba.