Yan sanda sun ceto ɗaliban firamare 2 daga cikin 6 da aka sace a Nasarawa

Rundunar yan sandan jihar Nasarawa ta ce jami’anta sun samu nasarar ceto yara biyu daga cikin ɗaliban firamaren dake Alwaza a karamar hukumar Doma ta jihar.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar,Ramhan Nansel shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.

Kafar yada labarai ta Arewa.ng ta bada rahoton yadda wasu yan bindiga suka sace ɗaliban makarantar firamaren su 6 da safiyar ranar Juma’a.

Nansel ya ce an ceto yaron nan a kauyen Sabon Kwara dake karamar hukumar Obi ta jihar inda suke samun kulawa a asibiti.

Ya kara da cewa ana cigaba da kokarin ceto sauran yaran huɗu da haɗin gwiwar sauran jami’an tsaro.

More from this stream

Recomended