Yan sanda a Lagos sun kama mutane biyu dake yin jabun lemon kwalba

Rundunar yan sandan jihar Lagos, ta kama wasu mutane biyu da ake zarginsu da yin jabun lemukan kwalba.

Mutanen biyu da suka fada komar yan sanda sun hada da Imo Lawrence mai shekaru 35 da kuma Magnus Nwanka mai shekaru 42.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Lagos, Benjamin Hundeyin ya ce wadanda ake zargin sun yi wa jami’an yan sanda jagora ya zuwa wurin da suka aikata laifin.

“jami’an yan sanda na ofishin Ojo sun kama mutane biyu, Lawrence mai shekaru 35 da Magnus Nwanka mai shekaru 42 dauke da jabun abun sha”

“A cigaba da bincike wadanda ake zargi sun yi wa yan sanda masu bincike jagora zuwa masana’antarsu da ba a iya gane ta inda take dauke da dakuna da dama” a cewar Hundeyin.

A wani bidiyo da mai magana da yawun rundunar yan sandan ya wallafa ya nuna dakuna makare da lemukan kwalba iri daban daban.

More from this stream

Recomended