
Rundunar yan sandan jihar Kebbi tace jami’anta sun kama wasu motoci biyu da suke dauke da harsashi 7500 da kuma kunshin ganyen tabar wiwi da kudinsu ya kai miliyan N600.
Nafiu Abubakar mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ya ce É—aya daga cikin motocin ta taso ne daga Ghana ta biyo Togo da Jamhuriyar Benin kana ta shigo Najeriya.
Ya kara da cewa mota ta biyu ta taso ne daga jamhuriyar Benin.
“A ranar 10 ga watan Satumba tawagar yan sanda dake sintiri akan iyaka akan titin Saransa zuwa Maje a karamar hukumar Bagudo sun kama babbar motar kwantena da aka yiwa rijista Lagos IT 21520 LA tana dauke da kunshi 4927 na ganyen da ake zargi tabar wiwi ce” ya ce.
” Mutane uku ake zargi Emmanuel Chukwuma daga jihar Abia, Kanta Bisa daga Ghana da kuma Shola Adeyemi daga Ondo su ne aka kama a yayin da sauran suka tsere”
Ya kara da cewa jami’an yan sandan sun sake kama wata mota mai namba IT 21608 dauke da harsashi 7500 da kunshin busasshen ganye da ake zargin na tabar wiwi ne.