Hukumar NMDPRA dake lura da tacewa tare rarraba man fetur da iskar gas ta rufe gidan man Botoson Oil and Gas LTD dake jihar Taraba.
A cikin wata sanarwa hukumar ta NMDPRA ta ce ta rufe gidan man ne bayan da aka same shi da karkatar da mota 18 ta man fetur ya zuwa kasuwar bayan fage.
Dukkanin man fetur da aka tura gidan man daga ranar 4 ga watan Afrilu ya zuwa ranar 5 ga watan Mayu bai samu isa gidan man ba ma’ana dai ya yi ɓatan dabo.
Gidan man na Botoson Oil and Gas na garin Mararaba Baisa dake ƙaramar hukumar Kurmi ta jihar Taraba.
Rufe gidan man na zuwa ne dai-dai lokacin da ake cigaba da samun tsada da kuma dogayen layukan mai a sassa daban-daban na ƙasarnan.