Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wasu katan 820 na wasu da ake zargin jabun magunguna ne wadanda kuma wa’adinsu ya ƙare a kasuwar Mallam Kato da ke karamar hukumar Fagge a jihar.
A cewar wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna, ya fitar a ranar Asabar, ya ce an gano magungunan ne a wasu shaguna biyu a kasuwar.
Ya ce magungunan sun hada da katon 514 na eemistxmin/emstifer syrup, kwali 219 na 5mg Lisinopril tablets, katan na 5mg amlodipine tablets, cartons na 50mg atenol da kwali 40, kwali 3 na allurar Frusemide.
Haruna ya ce, an kwashe magungunan ne aka mika su ga hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa ta hannun tawagar jami’an ‘yan sanda da kwamishinan ‘yan sandan jihar, Usaini Gumel, ya tura wurin.
Ya kuma umarci mazauna garin da su rika kai rahoton mutanen da suke zarginsu da kuma abubuwan da suka saba wa ‘yan sanda domin daukar matakin gaggawa.