‘Yan matan Chibok: Cameron ya yi min kage, inji Goodluck Jonathan

Goodluck E. Jonathan yana jawabi a wurin taro

Hakkin mallakar hoto
@GEJonathan

Image caption

Goodluck Jonathan ne shugaban Najeriya a lokacin da aka sace ‘yan mata daga makarantar sakandare a garin Chibok na jihar Borno

Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ya ce zargin da tsohon Firaministan Birtaniya David Cameron ya yi masa na cewa shi ne ya hana ceto ‘yan matan Chibok “zuki ta malle ne kawai”.

David Cameron, wanda shi ne Firaministan Birtaniya a lokacin da abin ya faru, ya yi zargin cewa Shugaba Goodluck Jonathan ne ya kawo wa gwamnatin Birtaniya tsaiko wajen ceto ‘yan matan a lokacin da yake shugaban Najeriya.

Cameron ya yi zargin ne a wani littafi da ya wallafa mai suna For The Record.

Ya ce: “Mun hango ‘yan matan na Chibok daga sama a wani kasurgumin daji….amma da alama Shugaban Najeriya (na lokacin) Goodluck Jonathan likimo yake yi kuma a karshe da ya farka sai ya zargi kungiyar rajin ceto ‘yan matan da laifin siyasantar da al’amarin.

“Duk da irin muhimmancin abin, da muka bukaci mu ceto su sai ya ki yarda.”

Wannan zargin na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan matan na Chibok ke cika kwana 2,000 da sacewa.

A martanin da ya mayar wa Mista Cameron a shafinsa na Facebook, Goodluck Jonathan ya ce ya yi mamaki matuka kan kalaman nasa, kuma ya ce ya tabbatar da cewa ba shi kadai ne yake jin cewa Cameron ya sharara karya ba.

“Ba zan zama mutum na farko ba da yake kallon wadannan kalamai a matsayin zancen kawai, sannan kuma ganin yadda mutane suke yin martani a Birtaniya ma tabbas ba zan zama na karshe ba,” in ji Jonathan.

Ya kara da cewa: “Abin takaici ne Mista Cameron ya rika fadar irin wadannan abubuwa saboda duk cikinsu babu wanda ya faru.

“A matsayina na shugaban Najeriya, na rubuta wa David Cameron wasika da Barrack Obama na Amurka da kuma shugaban Faransa François Hollande har ma da na Ira’ila Benjamin Netanyahu duka domin nerman taimakonsu wajen ceto ‘yan matan nan.

“Ta yaya zan nemi a taimaka mani sannan kuma na ki karbar taimakon?”

Hakkin mallakar hoto
@GEJonathan

Jonathan ya kuma ce tarihi ma ya karyata Mista Cameron domin kuwa lokacin da yana Shugaban Najeriya shi ne da hannunsa ya bai wa sojojin Birtaniya damar shiga jihar Sokoto domin ceto wasu ‘yan Birtaniyar da aka sace a watan Maris na 2012.

More News

Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan...

An ceto mutane 9 daga wani ginin bene da ya ruguzo a jihar Niger

Mutane 9 aka samu nasarar cetowa daga wani ginin bene mai hawa É—aya da ya ruguzo a yankin Sabon Gwari dake garin Minna babban...

An yi faÉ—a tsakanin masu sayar da waya da sojoji a kasuwar Abuja

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, ta tura jami’an leken asiri zuwa kasuwar Banex – wata kasuwar kayan lantarki da na’urorin sadarwa da ke...

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...