‘Yan majalisa sun amince Birtaniya ta fice daga EU da gagarumin rinjaye

Boris Johnson

Majalisar dokokin Birtaniya ta jefa kuri’ar amincewa da dokar ficewar kasar daga Tarayyar Turai bayan kusan shekaru 50, da gagarumin rinjaye.

Kwanaki takwas bayan lashe zaben Jam’iyyar Conservative ta Boris Johnson ya kawo karshen tayar da jijiyoyin wuya ake yi kan batun a majalisar tun bayan kuri’a raba gardamar da aka yi a 2016.

‘Yan majalisar shida daga jam’iyyar adawa ta Labour sun goyi bayan gwamnati a kuri’a, suna cewa sun amsa kiran da mazabunsu suka yi musu na su amince da ficewar kowa ya huta.

Yanzu dai za a tura dokar zuwa majalisar dattawa domin su yi muhawara a kai kafin gwamnati ta shiga tattaunawa da EU din don daddale magana kan ficewar.

More News

Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan...

An ceto mutane 9 daga wani ginin bene da ya ruguzo a jihar Niger

Mutane 9 aka samu nasarar cetowa daga wani ginin bene mai hawa É—aya da ya ruguzo a yankin Sabon Gwari dake garin Minna babban...

An yi faÉ—a tsakanin masu sayar da waya da sojoji a kasuwar Abuja

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, ta tura jami’an leken asiri zuwa kasuwar Banex – wata kasuwar kayan lantarki da na’urorin sadarwa da ke...

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...