‘Yan garkuwa da mutane sun sako babar Siasia | BBC Hausa

Samson Siasia

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Wadanda suka yi garkuwa da mahaifiyar tsohon kocin tawagar kwallon kafar Najeria, Samson Siasia sun sako ta bayan wata 10 da ta yi a hannunsu.

Tun a cikin watan Yuli aka sace Uwargida Ogere Siasia mai shekara 76 tare da wasu mutum biyu a jihar Bayelsa, kudancin Najeria, yankin da ake yawan garkuwa da mutane don kudin fansa.

Siasia wanda ya yi rokon a sakar masa mahaifiyarsa a makon jiya, ya shaidawa BBC cewar yanzu hankalinsa ya kwanta tun da ta dawo cikin iyalanta da koshin lafiya.

A sanyin safiyar Lahadi aka saki Ogere, sai dai ba a fayyace ko an biya kudin fansa ba.

Wannan ne karo na biyu da aka kama mahaifiyar Siasia, bayan da aka taba dauke ta har ta yi kwana 12 daga baya aka sake ta cikin Nuwambar 2015.

Tsohon dan kwallon tawagar Najeriya, Siasia ya daukaka kara kan dakatar da shi da Fifa ta yi daga shiga sabgogin tamaula har abada, kan zargin cuwa-cuwar sayar da wasanni.

Ana sa ran zai biya Dalar Amurka 100,700 nan da ranar 10 ga watan Oktoba kan kotun sauraren daukaka kararrakin wasanni ta duniya ta zauna kan batunsa.

Siasia ya buga wa Najeriya wasa sama da 50 ya kuma ci kwallo 16, ya lashe kofin nahiyar Afirka a 1994, sannan ya buga kofin duniya da aka yi a Amurka a shekarar.

A matsayinsa na koci ya yi nasara a jan ragamar tawagar matasan Najeria ‘yan 20 a shekarar 2005 da ta ‘yan 23 a 2015.

Ya kuma yi na biyu a gasar kwallon kafa ta matasa ‘yan shekara 20 a gasar duniya da aka yi a Netherlands.

Shi ne kocin da ke kan gaba a taka rawar gani a Afirka a gasar Olympics bangaren kwallon kafa, inda ya lashe azurfa a Beijing a 2008 da tagulla a Rio, Brazil a 2016.

More News

Ƴan Fashin Daji Sun Kashe Mutane 7 A Jihar Kebbi

Mutane 7 aka bada rahoton ƴan fashin daji sun kashe  a garin Tudun Bici dake ƙaramar hukumar Danko Wasagu ta jihar Kebbi. A cewar mazauna...

Tsoffin gwamnoni sun wawashe sama da naira tiriliyan 2 tun komawa dimokuraÉ—iyya

Aƙalla tsoffin gwamnoni 58 ne ake zargin sun wawure kuma sun yi almubazzarancin jimillar naira Tiriliyan 2.187 a cikin shekaru 25 tun komawa mulkin...

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar Æ´an sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...