Magoya bayan jam’iyyar NNPP da dama ne suka jikkata a wasu farmaki da yan bangar siyasa suka kai musu a Kano.
An kai harin ne a dai-dai lokacin da yan jam’iyyar suka fara yin dafifi domin tarar ɗan takarar shugaban kasa a jam’iyar ta NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso inda yake komawa gida Kano bayan kammala yaƙin neman zaɓe.
Tun da farkon safiya ne rahotanni suka bayyana cewa ana zargin jam’iyyar APC mai mulkin jihar da tara yan daba inda aka jibge su a wasu wurare da dama domin tayar da zaune tsaye a yayin ziyarar.
Ababen hawa da dama aka lalata a yayin fadan tare da jikkata wasu mutane da dama.





