‘Yan bindiga sun kai hari garin Nasarawar Mai-fara a yankin karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara

‘Yan bindiga sun kai hari garin Nasarawar Mai-fara a yankin karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara, inda suka halaka mutum fiye da ashirin, bayan da suka sara wa jama’ar kauyukan wajen tarar zaman lafiya naira miliyan 40.

Wani mutumin Nasarawar Mai-fara ya shaida wa BBC cewa a daren ranar Jumma’a ne aka yi jana’izar mutanen da ‘yan bindigar suka halaka a harin bazatar da suka kai.

Mutumin ya ce kafin wannan iftila’in ya same su sai da ‘yan bindigar suka zo suka ce su hada kudi su mazauna yankunan domin siyan zaman lafiya, haka kuma aka yi suka tara naira miliyan 40 suka basu.

To amma sai gashi ba zato ba tsammani suka shigo musu garuruwa suka fatattake su bayan kashe musu mutane fiye da 21, in ji mutumin.

Ya ce,” Abin takaicin ma shi ne bayan sun kashe mana mutane sai da aka kwana biyu sannan suka bar mu muka je muka dauko gawawwakin aka yi musu sitira”.

A garin ‘yar Katsina dake yankin karamar hukumar Bingudu a Zamfarar ana gab da sallar Jumma’a ne maharan suka kai hari garin.

Wani daya tsallake rijiya da baya a harin ya shaida wa BBC cewa, suna shigowa garin suka nufi masallaci suka bude wuta nan aka fara dauki ba dadi tare da ‘yan sa kai da ke garin.

Mutumin ya ce,”Da muka abin ba sauki muka kira jami’an tsaro su zo ba suzo ba har sai da ‘yan bindigar suka shafe sa’a biyu da rabi ana harbe- harbe da su”.

A wannan hari an kashe mutum 11, tare da raunata wasu mutum hudu, sannan an yi awon gaba da mata da dama in ji mutumin.

Su kuwa jama’ar garin Tofar Magami a yankin karamar hukumar Gusau ta jihar Zamfarar, gudun hijra suka yi in da ‘yan bindigar suka kankane garin.

Wani daasalin garin da suka yi gudun hijra ya shaida wa BBC cewa a halin da ake ciki yanzu a garin nasu ba bu mutum ko guda, barayin dajin ne suka kankane tare da kafa sansani.

Mutumin ya ce,”A yanzu haka barayin na zaune a cikin gidajen mutanen da suka tsere, kuma irin wulakancin da suke mana a yanzu bayan kashe mana mutane su duake su har ta kai yanzu ma a gabanka za a yi lalata da matarka kana gani”.

A nasu bangaren rundunar ‘yan sandan jihar ta bakin jami’in hulda da jama’arta SP Muhammad Shehu, ya shaida wa BBC cewa, ba suyi kasa a gwiwa ba wajen zuwa su jajantawa wadanda wannan lamari ya shafa.

Ya ce, an hada tawagar jami’an tsaro mai karfi aka kai wannan ziyarar jaje, sannnan kuma an tabbatarwa da mazauna garuruwan cewa ana nan na ci gaba da daukar matakan da ya dace wajen magance harin ‘yan bindigar.

More News

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...

ÆŠan agajin Izala ya samu lambar yabo, kujerar hajji, kyautar mota bayan ya tsinci naira miliyan 100 ya mayar wa mai su

Salihu AbdulHadi Kankia, mamba ne na kungiyar agaji ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), ya samu yabo da tukuicin mayar da...