‘Yan bindiga Sun Sace Ma’aikata Da Jariri Daga Wani Asibiti a Zariya

VOA Hausa

A yayin da kuma lokaci guda suka kai hari ofishin’ yan sanda da ke kusa, a cewar ’yan sanda da jami’an asibitin.

Jihar Kaduna ta sha fama da sace-sacen mutane don neman kudin fansa daga hanun ‘yan bindiga. A Zariya, inda asibitin tarin fuka da cibiyar kuturta ta ke, an fi samun hare-hare, kuma wannan harin shi ne na uku a asibitin.

Harin da sanyin safiyar ranar Lahadi ya dauki kimanin awa daya, kamar yadda mai magana da yawun asibitin Maryam Abdulrazaq ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Ta ce an sace mutane shida: ma’aikatan jinya biyu, daya da danta mai shekara daya, da wani kwararre mai gwaje-gwaje, da jami’in tsaro da kuma wani ma’aikaci guda. ‘Yan sanda sun ba da adadin wadanda aka yi garkuwar da su har takwas.

Abdulrazaq ta ce “Ya zuwa yanzu, basu nemi kudin fansa ba,” “Ba mu sake jin labarin ‘yan fashin ba tun da suka tafi da su.”

A wata sanarwa ta daban, kakakin rundunar ‘yan sanda na Kaduna, Muhammed Jalige ya ce“ wasu ‘yan bidiga da yawa dauke da muggan makamai daga wannan kungiya sun kai hari hedkwatar’ yan sanda na shiyya a daidai lokacin guda “a kokarin mamaye jami’an da ke bakin aiki.”

Jalige ya ce ‘yan sanda sun dakile harin bayan musayar wuta da aka yi, wanda ya raunata wasu daga cikin maharan. ‘Yan sanda sun kwato harsasai da yawa daga bindigogi da manyan bindigogi.

Ya ce jami’ai daga bangaren dabaru, masu yaki da satar mutane da sauran bangarori na aiki don ceto wadanda aka sace daga asibitin.

Satar mutane domin neman kudin fansa ta zama ruwan dare a arewacin Najeriya. Fiye da dalibai 800 aka sace tun watan Disamba, akalla 150 daga cikinsu sun kasance a bace ya zuwa yanzu.

More News

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...