‘Yan bindiga sun kona gidan mai garin Babban Gida

Wata mota mai dauke da tutar kungiyar IS

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Da rana ne ‘yan bindigar suka garin

Rahotanni daga garin Babban Gida na karamar hukumar Tarmuwa da ke jihar Yobe na cewa wani gungun ‘yan bindiga ya shiga garin, inda suka rika harbe-harbe har ma suka cinna wa gidan mai gari wuta.

Da misalin karfe 2:00 zuwa 3:00 na rana ne dai ‘yan bindigar da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne suka shiga garin, kamar yadda wasu mazauna garin suka ya shaida wa BBC.

Zuwa yanzu dai babu tabbacin yawan wadanda suka rasa rayuka amma rahotanni na cewa wata mata ta rasu sannan kuma an jikkata wani mutum daya.

‘Yan bindigar kuma sun cinna wa gidan mai garin Babban Gida wuta.

Kawo yanzu dai jami’an tsaro ne ke zagaye da gidan, yayin da su kuma ‘yan bindigar aka daina jin duriyarsu.

Mutane sun ci gaba da harkokinsu bayan sallar magariba.

Kwana biyar da suka gabata kamfanin dillanci labarai na Reuters ya ruwaito cewa kungiyar Boko Haram ta halaka akalla mutum tara a wani hari da ta kai garin Gubio da ke jihar Borno.

Kafar ta Reuters ta sake wallafa rahoto a ranar Litinin cewa kungiyar IS ta fitar da ikrarin cewa ta kai harin kuma ta kashe da jikkata sojoji da dama.

More from this stream

Recomended