Yan bindiga sun kashe sama da mutane 40 a Katsina – AREWA News

Sama da mutane 40 aka kashe a jihar Katsina a wani hari da ake zargin yan bindiga da kai wa a jihar.

Wata majiya dake jami’an tsaro ta bayyana cewa maharan sun kai farmaki ne kauyen Kadisau dake karamar hukumar Faskari ta jihar.

Majiyar ta ce bayan cews da suka farma Kadisau sun rika bi gida-gida suna harbe duk wanda suka ci karo da shi.

“Harin ya fara ne da misalin karfe hudu na yammacin jiya kuma sun dauki sa’o’i suna kisa tare da kunnawa gine-gine wuta,” ya ce.

“Yan bindigar sun tafi a kashin kansu bayan awanni da dama, jami’an tsaro sun zo kauyen. Baki dayan wurin babu kowa saboda wadanda suka tsira sunyi tattaki ya zuwa garin Funtua.”

Wasu daga cikin wadanda suka samu raunuka na cigaba da samun kulawa a asibitin Funtua.

More from this stream

Recomended