Gwamnan Jihar Neja a arewacin Najeriya ya ce ‘yan bindiga sun kashe mutum aƙalla 220 a jiharsa cikin wannan watan na Janairu kaɗai a hare-haren da suka kai yankuna 300.
Da yake magana da manema labarai jim kaɗan bayan ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari a Abuja ranar Talata, Gwamna Abubakar Sani Bello ya ce cikin waɗanda aka kashe akwai jami’an tsaro 25 da kuma ‘yan sa-kai 30.
Ya ƙara da cewa ‘yan bindigar da ake yi wa laƙabi da ‘yan fashin daji sun sace mutum 200 a watan na Janairu.
Kalaman gwamnan na nuna yadda matsalar tsaro ta ta’azzara a jihar, wadda hare-haren ‘yan bindigar da ke sace mutane don neman kudin fansa suka addaba.
A ranar Litinin ne gwamnatin Najeriya ta ce ta ƙaddamar da “gagarumin aikin sojoji a jihar Neja”.