Yan bindiga sun kashe mutane 4 Bauchi

Rundunar yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da kisan mutane 4 da wasu yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka yi a kauyen Gambar Sabon-Layi dake ƙaramar hukumar, Tafawa Balewa dake jihar.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, SP Ahmed Wakili shi ne ya tabbatar da haka a wata ganawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ranar Lahadi.

Ya ce yan bindigar sun kai hari kauyen da daddare inda suka sace mutum guda.

Ya ce tuni kwamishinan yan sandan jihar ya bayar da umarnin gudanar da bincike domin kama wadanda suka aikata kisan.

More from this stream

Recomended