‘Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 6 a Anambra | BBC Hausa

Dakarun Nijeriya
Bayanan hoto,
Dakarun Nijeriya

Jami’an tsaro akalla shida ne suka hallaka a jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya.

Jami’an tsaron sun hada da sojojin ruwa uku da wasu yan bindiga suka harbe a garin Awkuzu da ke karamar hukumar Oyi.

Sai kuma jami’an ‘yan sanda uku da yan bindigar suka harbe a Neni da ke karamar hukumar Anaocha tare kuma da cinna wa motarsu wuta.

Al’amarin ya janyo zaman zulumi a jihar kuma ana rade radin cewa an sami wani gungun ‘yan bindiga da ke kai wa jami’an tsaro hari a jihar ta Anambra.

Rahotanni sun ce yan bindigar sun harbe sojin ruwan ne da karfe biyu na rana inda suka yi awon gaba da makamansu.

Jihar Anambra na cikin jihohin da aka hallaka jamian’yan sanda tare da kona caji ofis na yan sanda a watan Fabarerun daya gabata.

More News

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...