Yan bindiga sun kashe DPO a Anambra

Da tsakar daren ranar Litinin yan bindiga sun kai hari ofishin yan sanda na Isiowulu dake Awada a karamar hukumar Idemili North dake jihar Anambra inda suka kashe DPO da wasu mutane biyu.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa yan bindigar masu yawan gaske sun farma ofishin yan sandan da misalin karfe 02:18 na dare inda suka rika musayar wuta da yan sanda.

Yan sandan tare da taimakon sojoji sun samu nasarar dakile kai harin tare da kashe uku daga cikin yan bindigar.

DPO taren da wani sabon Konsitebulari da kuma Insifecta su ne suka mutu a harin.

More from this stream

Recomended