‘Yan bindiga sun hallaka ‘yar Birtaniya a Najeriya

Faye Mooney

Hakkin mallakar hoto
YouTube

Image caption

Wata ‘yar Birtaniya na cikin mutum biyu da masu satar mutane domin kudin fansa suka kashe a wani wurin shakatawa a Najeriya.

Ofishin jakadancin Birtaniya a Najeriya ya tabatar da aukuwar lamarin, wadda kungiyar da ta ke wa aiki ta bayyana cewa sunanta Faye Mooney.

Kungiyar mai suna Mercy Corps ta ce Faye Mooney na aiki ne a Najeriya, kuma abin takaici ya faru a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka far ma wurin da ta ke hutunta a jihar Kaduna da ke arewacin kasar.

‘Yan sanda a jihar ta Kaduna sun tabbatar da mutuwar wani dan Najeriya, bayan sace wasu mutum uku da maharan suka yi a ranar Jumma’a.

Satar mutane domin karbar kudin fansa ya zama ruwan dare gama duniya a Najeriya, inda ake farautar ‘yan kasashen waje da manyan ‘yan Najeriya.

More from this stream

Recomended