Yajin aikin ASUU: Malaman jami’a sun ce ba za su koma aiki ba sai an biya su albashinsu

ASUU and Labour Ministry meeting on top di ongoing strike

Kungiyar malaman jami’a ta Najeriya ASUU, za ta kammala tattaunawar da take yi a wannan makon sannan ta sanar da gwamanti domin su sake zama.

ASUU na tattaunawa da sauran mambobinta kan sabon tayin da gwamnati ta yi musu bayan kammala tattaunwarsu a ranar 27 ga watan Nuwamba.

A tattaunawar da aka yi, gwamnati ta yarda ta biya malaman albashinsu amma sai sun fara komawa bakin aikinsu – abin da malaman suka ce sun Æ™i wayon, babu kudi babu aiki.

Sun ce kada ma gwamnati ta za ci wani zai koma koyarwa matukar ba a biya su kuÉ—aÉ—ensu ba.

Kungiyar na kukan cewa gwamnati ta riÆ™e albashin ‘ya’yanta saboda ta Æ™i shiga cikin tsarin biyan albashin bai É—aya da gwamnatin ta Æ™addamar.

“Yana da matukar muhimmanci a san cewa gwamnati ta rike wa mambobinmu alawus-alawus da kuma albashinsu tun daga watan Yuli 2020 har zuwa watan Oktoba 2020, kimanin watanni huÉ—u kenan,” in ji wani shugaban shiyya Olusiji Sowande da ya shaida wa BBC.

Uwar kungiyar ta Æ™asa ta ce, gwamnati ta É—ibar musu wani wa’adi da za ta biya albashinsu tare da kuma bibiyar yadda za a biya kuma wa’adin zai kare ne a karshen wannan makon, sannan sai kungiyar ta dauki mataki na Æ™arshe.

Sun ce matukar gwamnati ba ta biya albashinsu ba, ba za su koma makaranta ba, kuma sun daina amincewa da duk wani alkawari da gwamnatin za ta yi musu a nan gaba.

Wakilan bangarorin biyu sun haÉ—u sau bakwai domin samun mafita kan wannan yajin aiki, tare da bai wa dalibai damar koma wa karatu.

Kungiyar dai ta fara yajin aikin nata ne a watan Maris din wannan shekarar da nufin matsawa gwamnati ta samar da kayyyakin aiki a jami’o’i domin bai wa É—alibai damar koyo da kuma gogayya da takwarorinsu na ko ina a duniya.

Suna kuma buƙatar a biya su alawus-alawus dinsu wanda suka yi aiki ba a biya su ba.

Sai kuma abu na uku wanda shi ne biyan albashinsu da gwamnati ta riƙe musu.

Yajin aikin da aka kwashe wata takwas ana yi, an cimma wasu daga cikin buƙatun daga karshen tattaunawar tasu kamar haka:

  • Kungiyar na son gwamnati ta biya naira biliyan 110 domin gyara makaranta amma ta rage buÆ™atarta zuwa naira biliyan 55 amma gwamnati ta ce naira biliyan 30 kawai za ta iya biya
  • Gwamnati ta ce za ta biya naira biliyan 40 na alawus da sika ce suna bi
  • Game da albashinsu, gwamnati ta yarda ta biya a kan tsohon tsarin da ake biyansu
  • A karshen tattaunawar da aka yi gwamnati ta yarda ta biya ASUU kudin gyara jami’o’i, da suka kai naira biliyan 70.

To mene ne ya yi wa ASUU saura?

ÆŠaya daga cikin tayin da gwamnati ta yi wa ASUU da bai yi mata É—aÉ—i ba, shi ne kudin da ta ce za ta bayar domin gyaran jami’o’i.

BBC ta gano cewa da yawan makarantu a Najeriya na koken ba su da kayan aiki yadda ya kamata.

Suna cewa ba su da É—akunan karatu masu kyau, babu wuta wasu ma ba su da kujeru.

Sun ce dakunan kwanan É—alibai sun lalace, da kudin da gwamnati ta bayar ba za a iya shawo kan wadannan matsaloli ba da jami’un Najeriya ke fama da su.

Abu na biyu, shi ne maganar albashinsu, wanda gwamnati ta ce su fara komawa bakin aiki kafin ta biyasu, sai dai sun ce a biya su sai su koma makaranta.

Wannan gwamnati ba da gaske take ba, ta kuma nuna wa ASUU ba za ta iya cika alkawarinta ba.

“Ngige na wajen da aka cimma yarjejeniya a 2017 haka ma a 2019 har zuwa yau, kuma bai cika jarjejeniyar ba dan haka ba za mu amince da su ba,” in ji wani shugaban ASUU.

Anya za a koma makaranta a wannan shekarar?

Har yanzu babu wani tabbaci kan buÉ—e jami’o’i a Najeriya.

Har yanzu dai akwai wasu matsalolin da É“angarori biyun ba su cimma matsaya a kansu ba.

Tun daga shekarar 1978 da aka ƙirƙiri kungiyar ASUU, kungiyar ta je yajin aiki da dama domin samun biyan bukatunta.

Ta je yajin aiki a shkerun 1988 da 1992 da 2007 da 2008 da 2009 da 2013 da 2017 da 2019 da kuma 2020 tare da kawo ƙarshensu, amma a wannan karon sun ce ba za su koma ba har sai an biya musu bukatunsu.

(BBC Hausa)

More News

Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan...

An ceto mutane 9 daga wani ginin bene da ya ruguzo a jihar Niger

Mutane 9 aka samu nasarar cetowa daga wani ginin bene mai hawa É—aya da ya ruguzo a yankin Sabon Gwari dake garin Minna babban...

An yi faÉ—a tsakanin masu sayar da waya da sojoji a kasuwar Abuja

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, ta tura jami’an leken asiri zuwa kasuwar Banex – wata kasuwar kayan lantarki da na’urorin sadarwa da ke...

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...