Yadda za ku kauce fada wa rikici da ‘yan sandan Najeriya a kan hanya | BBC Hausa

Kunna fitilar mota a lokacin da direba ya zo gaban shingen bincike na kan hanya na taimakawa wajen samun kyakkawar fahimta tsakanin 'yan sanda da direbobi

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Kunna fitilar mota a lokacin da direba ya zo gaban shingen bincike na kan hanya na taimakawa wajen samun kyakkawar fahimta tsakanin ‘yan sanda da direbobi

Yin murmushi da da’a da kuma gudun yin fada da dan sanda na cikin abubuwan da ke taimakawa direba a duk lokacin da ya zo gaban shingen bincike na ‘yan sanda kamar yadda rundunar ta wallafa a shafinta na Twitter.

Ba a bayyana takamaiman dalilin da ya sa rundunar ‘yan sandan ta wallafa wadannan shawarwarin amma ana ganin an wallafa ne sakamakon wani bidiyo da yake yawo a shafukan sada zumunta na wani dan sanda na da ke cin mutuncin wani direba.

A cikin bidiyon, an nuna wani dan sanda inda ya bukaci a ba shi cin hancin naira 4,000 saboda abin da direban ya yi niyyar ya ba shi bai kai hakan ba.

Irin wadannan lamuran sun sha jawo a harbe direbobi su mutu sakamakon kin bayar da kai bori ya hau.

‘Yan sandan ba su yi magana a kan karbar cin hanci ba, amma a shawarwarin da suka bayar na mu’amala cikin mutunci da ‘yan sanda a yayin da aka same su a gaban shingen bincike na kanya sun bayar da shawarar cewa:

”A lura da suna ko lamba ko kuma motar jami’an tsaro a duk lokacin da suka nuna alamun yin wani abu da ya saba ka’ida.”

Idan kuna tunanin yadda za ku bi wadannan shawarwarin, ga abin da ya kamata direbobi su yi:

A rage gudun mota idan aka dumfari shingen bincike, a tabbatar da cewa an kunna fitilar mota idan da dare ne, kada a boye hannuwa domin hakan na iya fusata ‘yan sanda.

”Za a so a rage sautin rediyo a duk lokacin da aka kusanci shingen bincike, yin hakan zai iya bayar da dama a fahimci juna idan ana magana kuma hakan zai iya sa wa ‘yan sandan su yarda da mutum.”

Fusata dan sanda ba shawara mai kyau ba ce:

”Sau da dama za a ji mutane na fadin abubuwa kamar a harbe ni, a sani cewa wannan na iya jawo matsala, wannan na harzuka ‘yan sanda kuma na jawo rikici, a bi a hankali domin ba a san yanayin da wani dan sanda yake ciki ba.”

Hakazalika taba dan sanda:

”Akwai dubban hanyoyi da za a iya bi domin bin kadin abubuwan da ake gani an take wa mutum hakki, kada a kuskura a taba dan sanda ta hanyar da bata da ce ba, dan sandan zai iya zargin za a yi kokarin kwace masa bindiga ne.”

Rundunar ‘yan sandan ta ga cewa yakamata ta bayyana illoli da kuma irin abubuwan da za su iya biyowa bayan fada da dan sanda mai rike da makami ko bindiga:

”Kada a ce za a yi fada da jami’in dan sanda mai rike da makami domin zai iya amfani da makaminsa domin kare kansa. A guji gardamar da ba ta da amfani da ‘yan sanda.”

Akasarin ‘yan Najeriya ba su amince da ‘yan sanda ba domin suna ganinsu a matsayin masu cin hanci da rashawa da kuma sabawa doka kamar yadda Editan BBC na Najeriya Aliyu Tanko ya bayyana.

‘Yan kasar na yawan kokawa dangane da yawan shingayen bincike na kan hanya inda suke ganin kamar an kafa su ne domin karbar cin hanci.

Wakilin BBC ya bayyana cewa ‘yan sandan Najeriya na daga cikin jami’an ‘yan sandan duniya da ba a biyansu albashi kuma ke fama da rashin ingantattun makamai.

Amma ‘yan sandan na ganin cewa rashin mu’amala ta gari da jama’ar gari suke yi da su ke jawo rashin fahimtar da ake yi masu.

‘Yan sandan sun bukaci jama’a da su rinka basu girmansu idan suna mu’amala da su.

”Mun san cewa aikinsu ne, amma kalamai masu dadi daga jama’a za su taimaka. A tuna idan aka yi wa madubi murmushi, shi ma zai yi maka murmushi.”

Ana ganin wadannan shawarwarin da rundunar ‘yan sandan ta wallafa a shafinta na Twitter, wani yunkuri ne na dawo da martabarta a idon mutane.

Wannan na zuwa ne bayan sunan ‘yan sandan ya ta yawo a kafafen sada zumunta.

More News

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

Sojoji sun gano masana’antar Æ™era bom a jihar Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun gano wata masana'anta da mayaƙan kungiyar ISWAP suke ƙera bama-bamai. Masana'antar ƙera bama-bamai an gano ta ne a Abulam-BUK dake...

Atiku ya ziyarci Abdul Ningi

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya ziyarci dakataccen ɗan majalisar dattawa sanata, Abdul Ningi dake wakiltar mazaɓar Bauchi ta tsakiya a majalisar dattawa. Atiku...