Sai dai hukumomin tsaro na ikirarin cewa suna samun nasara akan ‘yan fashin dajin a hare-haren da suke kai musu.
A daidai lokachin da gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da kashe wasu ‘yan-bindiga da kuma ceto mutanen da aka sace.
Al’ummar karamar hukumar Birnin Gwari sun ce bayan hare-haren ‘yan-bindigan da su ka yi sanadin tada garuruwa sama da tara cikin mako daya, a ranar Talata ma ‘yan-bindiga sun sake tare hanyar Kaduna-zuwa Birnin Gwari kuma sun sace mutane da dama.
Garuruwan da su hada da Kungin Dan-Bauchi, Kimbi Katagagi, Damari, Shirya, na cikin wadanda ‘yan-bindigan su ka tashi mutanensu baki daya cikin mako guda, kamar yadda Dan-masanin Birnin Gwari Alh. Zubairu Abdurra’uf Idris Birnin Gwari ya tabbatarwa Muryar Amurka.
“Wannan abu akwai ban takaici akwai ban tausayi, yadda wadannan mutane suka shigo a Waro, Rema, da unguwar Shehu da Sabon Gida, da dai wasu wurare a bangaren dagara inda wadannan ‘yan bindiga suka sace mata uku da mazaje wadanda ba’a son adadin su ba.”
Masana harkokin tsaro na ganin akwai gazawar gwamnati game da yaki da ‘yan-bindigan da su ka addabi al’umomi a yankin Arewa maso yammachin Najeriya. Dafta Yahuza Ahmed Getso na cikin masanan da ke da irin wannan hasashe.
“Idan muka kalli harin da aka kai a Birnin Gwari a jiya, ya tabbata cewar jami’an Najeriya ba su da makaman da za su iya tunkarar ‘yan ta’adda da ake da su wadannan yankunan musamman wannan hanya ta Birnin Gwari.”
Sai dai duk da matsalar hare-haren ‘yan-bindiga a wasu sassan jihar Kaduna, gwamnati ta ce jami’an tsaro na nasara akan su. Kamar yadda kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Kaduna, Malam Samuel Aruwan ya fada.
Da yawan masana harkokin tsaro dai na ganin muddin ba a afkawa ‘yan-bindigan da ke dazuzzukan Arewa maso yammacin Najeriya a lokachi guda ba, matsalar hare-haren ‘yan-bindiga ba za ta kawo karshe cikin takaitaccen lokaci ba.