Yadda ‘wani ya kashe abokinsa kan N500 a Kano’ | BBC Hausa

Habu Sani

Bayanan hoto,
Kwamishina Habu Sanine ya tabbatar wa da BBC labarin

Rundunar ƴan sandan jihar Kano a arewacin Najeriya ta tabbatar da mutuwar wani matashi mai shekara 22 da ake zargin wani abokinsa da kashe shi sakamakon wani saɓani da ya shiga tsakaninsu.

Yayin da yake tabbatar wa da BBC faruwar al’amarin, kwamishinan ƴan sandan jihar Habu Sani, ya ce wanda ake zargi da kashe Sani Ibrahim ya yi hakan ne a kan Naira 500, ta hanyar caka masa wuka a ƙirji, kuma hakan ya yi sanadin mutuwarsa.

To sai dai wani mazaunin unguwar da abun ya faru a kan idonsa Basiru Ahmad, ya ce daƙiƙa kaɗan kafin faruwar al’amarin, matasan biyu sun tsaya a wajensa har ya yi musu nasihar su zauna lafiya da junansu sannan suka tafi.

“Sun zo wajena mintina kaɗan kafin faruwar al’amarin, don mun gaisa da su har na yi musu fada cewa su zauna lafiya, babu hayaniya suna cewa da ni ai babu komai.

”Daga nan sai shi Sani Ibrahim ya je fitsari, to da yake gurin da duhu ban iya gane waye ya je inda yake fitsarin yake masa magana ba, sai na ga wani ma ya je kansa, daga nan sai jin ƙararsa muka yi su kuma waɗancan sun gudu”, a cewar Basiru Ahmad.

Wani daga cikin abokan mamacin Sani Alhassan ya ce suna gefe suna hira bayan dawowarsa daga sana’arsa ta tuƙa babur ɗin a-dai-dai-ta sahu, suka ga ana taruwa a inda aka kashe matashin, shi ne suka je suka tarar da Sanin a kwance ya dafe ƙirjinsa, yana faɗin sunan wanda ake zargi da kashe shi.

Me iyayen Sani ke cewa?

Zainab Isma’il ita ce mahaifiyar Sani, a hirarta da BBC ta nemi hukuma da ta bi mata hakkin ɗanta, wanda ta ce maraya ne kuma shi ke ɗawainiya da ita.

”Gani na da shi na ƙarshe shi ne lokacin da ya shigo don ya gaishe ni saboda ba ni da lafiya, daga nan sai ya cetun da bacci nake bari ya je ya dawo.

”Can kuma sai na ji ana sallama ana cewa wai in zo ga Sani can an caka masa wuƙa a ƙirji, shi ne na ce ba zan je ba su kawo min shi kawai don duk ƙirji makasa ne, kashe shi dama suka yi niyar yi, inji mahaifiyar ta Sani.

Malama Zainab ta ci ga da cewa: ”Shi kadai nake da shi kuma shi ke taimaka min, ya kan je Fatakwal yana harkar gwangwan ɗinsa, kuma da tuni ya tafi amma saboda rashin lafiyar da nake shi ya sa bai tafi ba ya ce sai na ji sauƙi.

“Dama suna yawan tsokanar sa, amma duk da na hana shi daka ta tasu su yi fada amma sai sun takale shi,” in ji mahaifiyarsa Sani.

Bayanan hoto,
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ana binciken lamarin a sashen binciken manyan laifuka

Tuni dai kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano Habu Sani ya tabbatar da kama wanda ake zargin, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike tare da mayar da batun sashen binciken manyan laifuka na rundunar yan sanda jihar.

A baya-bayan nan ma an samu rahoton yadda wani matashi mai suna Ashiru Danrimi mai shekara 22 da zargin ya kashe kansa, saboda budurwarsa ta zabi auren wani daban ba shi ba.

More from this stream

Recomended