Yadda mahara suka afka wa matafiya a Kaduna

Taswirar Kaduna

Wasu mahara da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun bude wa motocin matafiya wuta a jihar Kaduna jim kadan bayan sauka daga jirgin kasa a Rigasa.

Maharan sun yi ta harbin kan mai uwa da wabi lokacin da suka tare hanya da nufin yin awon gaba da fasinjoji.

Wasu bayanai sun tabbatar da cewa an kai harin ne da misalin karfe takwas da rabi na daren ranar Lahadi, lokacin da matafiya ke kokarin isa gidajensu bayan sauka daga jirgin kasa a tashar Rigasa.

Maharan sun bude wa motocin matafiyan wuta a yankin Mando, a kokarinsu na kama wasu daga cikin su ta hanyar tursasawa motocinsu tsayawa.

  • An harbo jirgin ‘yan sanda, an kashe ‘yan bindiga 250 a Kaduna
  • Yadda aka yi garkuwa da dalibai a Kaduna

Wani da ke cikin motocin da aka bude wa wutar ya shaida wa BBC cewa, “Muna cikin mota sai muka fara jin harbe-harbe, to ko da na daga kaina na kalli gabanmu sai na ga mutum biyu a tsaye da bindiga, to dama mota daya ce tsakaninmu da masu harbin, can sai aka ce mu juya masu garkuwa da mutane ne”.

Ya ce “Bayan mun juya mun tafi sai muka sake jin harbi ta bangaren hagu da damanmu, kamar dai kewaye mu suka yi. can sai na ji harsashin bindiga ya bugi kofar da nake a zaune, to amma bai same ni ba”

Mutumin ya ce akwai jami’an tsaro a hanyar amma kuma sai da suka bar inda jami’an tsaron suke sannan suka fara jin har bin bindigar.

BBC ta yi kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar kaduna kan wannan batun, sai dai ba ta ji daga gare su ba, sai dai wasu rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaro sun tarwatsa maharan a wannan lokaci.

Ba dai a samu bayani a kan rasa rai ko rauni a harin ba.

Karin bayani

Matsalar tsaro dai na ci gaba da karuwa a Najeriya a baya-bayan nan, domin bayan hare-haren kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin kasar.

Su ma masu garkuwa da mutane na ci gaba da tsananta ayyukan su a jihohin arewa maso yammacin kasar ciki har da jihar Kaduna da aka kai harin na yanzu.

A baya dai da yawan mutane na tunanin cewa shiga jirgin kasa ne hanyar samarwa kai kariya daga harin masu garkuwa da mutane, to sai dai harin na yanzu na iya jefa matafiya cikin halin gaba kura baya sayaki, domin tuni wasu da dama suka kauracewa bin hanyar Abuja zuwa Kaduna ta mota saboda gudun fadawa tarkon su.

Ko da a kwanakin baya ma an samu rahoton kai wa wani jirgin kasa da ya tashi daga Kaduna zuwa Abuja hari, abin da hukumomin Najeriyar suka musanta, tare da cewa yara ne suka jefi jirgin da dutse a lokacin da suke wasa.

More News

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...

Matatar Mai Ta Kaduna Za Ta Fara Aiki A Ƙarshen 2024

Kamfanin Kaduna Refining and Petrochemical Company KPRC ya ce matatar mansa za ta fara aiki a shekarar 2024. Mustapha Sugungun managan matatar man ta KRPC...

Manyan dillalan mai za su fitar da litar man fetur miliyan 300 a wannan makon

Ƙungiyar MEMAN ta manyan dillalan man fetur da dangoginsa ta ce mambobinta sun fara lodin mai har lita miliyan 300 a cikin makon nan...

Kotu ta É—aure mutumin sa ya yi sama-da-faÉ—i da kuÉ—in marayu

Babbar kotu a jihar Borno ta yanke wa Isiyaku Ibrahim hukuncin shekara ɗaya a gidan yari da zaɓin biyan tarar naira dubu 100 saboda...