Yadda kullen coronavirus ya janyo karuwar cin zarafi

An illustration of a caged woman seated on a couch

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cin zarafin mata a yayin kullen cutar korona a matsayin wata “boyayyar annoba”.

A fadin Afrika, gwamnatoci da ‘yan sanda da masu fafutuka na cewa cin zarafin mata manya da yara ya karu a lokacin da suke kulle a gida da mazansu ko ‘yanuwansu.

Don haka, me za ki yi idan kika samu kanki a wannan yanayi? Mun tambayi kwararru da wata wadda ta taba fuskantar cin zarafi don ba mu shawrwari.

“Ida nana cin zarafinki a gidan aurenki, za ki lura da wani salo,” Esther ta shaida min, da take tuna shekaru ukun da ta yi tare da mijinta da ke cin zarafinta a-kai-a-kai ta hanyra dukanta da zaginta.

“Duk karshen mako na kan shiga mawuyacin hali saboda kowa na gida. Wanda ke cin zarafinka na da lokaci sosai kuma zai ji ya gundura. Don haka sais u fara takalar fada. Su yi maki dabara – su fadi wani abu da zai tunzura ki kuma su dake ki idan kika rama.

‘Kamar an daure ni’

“Idan kwanaki biyu kawai na sa mutum ya ji ya gundura har ya ji yana so ya buge ki, to ya zai ji a wata guda ko fiye da haka? Wannan karon kuma ba gundura b ace kawai, fargaba ce da gajiya.”

An kwashe shekaru yanzu tun da Esther ta rabu da mijinta. Kuma duk da cewa a wancan lokacin ya fi mata sauki ta rabu da shi idan aka kwatanta da yanzu, sai da ta dau lokaci kuma ta samu kwarin gwiwa kafin ta rabu da shi.

“Na ji kamar ina gidan kaso kuma na kasa fita saboda rashin kudi sannan hankalina da zuciyata ba su gamsu in tafi ba a lokacin – sannan ga batun ‘ya’yana.

Sannan mahaifiyata na jin dadi ina zaune a gidan aurena, don haka don kada in bata mata rai, sai na zauna.”

Ga matan da ke son barin auren da ake cin zarafinsu a lokacin wannan kullen, suna da kalubale da yawa. Idan suka yi kokarin tafiya, ‘yan sanda na iya tare su saboda karya dokar hana fita kuma ba lallai su samu motar haya ba.

Kasashe da dama sun kaddamar da shirye-shirye don bai wa mutanen da ake cin zarafinsu shawarwari da tallafi kuma ana matukar kai kuka ga wadanann wurare.

‘An samu karuwar mutanen da ake cin zarafinsu’

A makon farko da dokar kullen ta fara aiki, ‘yan sanda a Afrika ta Kudu sun samu kararraki 2,320 kan cin zarafi tsakanin maza da mata – wannan ya karu da kasha 37 cikin 100 fiye da yadda aka saba.

A Zimbabwe, wani ofishi da ake tuntuba kan cin zarafi y ace yawan mutanen da ake cin zarafinsu da ya tattara ya rubanya sau uku, yayin da a Najeriya, wata mai fafutukar kare hakkokin jinsu, Dorothy Njemanze ta shaida wa BBC cewa tana fargabar karuwar da ake samu na mutanen da ake cin zarafinsu a kasarta: “Muna fargabar idan aka ci gaba a haka, za a samu mutanen da za su mutu kafin a dage wannan dokar kullen.”

Wasu kasashen Afrika na daukar matakan da suka dace don taimaka wa mata. A Tunisiya, kasar da ta kararrakin da a ke kaiwa kan cin zarafi ya rubanya sau biyar, gwamnati ta bude ofisoshi da lambobin waya da za a iya kira kyauta don kai karar cin zarafi kuma ta bude sansanoni takwas ga mutanen da suka tsere wa cin zarafi da ‘ya’yansu.

A wasu wurare, an bude sansanoni da yawa kuma ‘yan aikin sa kai na taimakawa mata tserewa daga irin wannan rayuwa.

A Zimbabwe, halin yanzu sansanin Roots One Stop na ajiye da manya 21 da yara bakawi. Shugabarta, Beatrice Savadye ta ce suna kokarin ceto mata daga gidajensu kuma ‘yan sanda na turo masu da wasu matan.

‘Bai wa mata mafaka’

A Kenya, mai aikin walwalar jama’a Dianah Kamande ta ce har yanzu sansanonin na iya bai wa mata mafaka kuma kungiyarta na ceto mata 17 a birnin Nairobi kawai.

A Najeriya, duk da cewa mafi yawan sansanonin da ke bai wa mata mafaka sun kulle saboda dokar hana fita da kulle da aka sa, masu aikin sa kai na iya taimaka wa mata tserewa zuwa wurin ‘yan uwansu a cewar Titilayo Vivour, mai kula da bangaren cin zarafi na jihar Legas.

Amma a Ghana, Shugabar sansanin Ark shelter, Nana Sunnu ta ce bas a iya bai wa wasu matan wurin zama saboda hadarin yada cutar korona da kuma rashin karfin iya killace su.

Esther, wacce ta tsere wa auren wahala kuma a yanzu take aiki da wasu irinta, ta ce mata su kira lambobin waya da ake warewa saboda cin zarafi ko da kuwa suna kasashen da aka rufe duka sansanonin.

“Ku yi kokari ku nemi masu fafutuka a shafukan sada zumunta, masu fafutukar da za ku iya amincewa da su. Ku kira su, akwai abin da za a iya yi ko a wannan lokaci na kulle.”

Al’uma ta sa ido kan makwabtan da suke tunanin ana cin zarafinsu, in ji masaniyar halayyar dan Adam Nthabiseng Ramothwala. Ta kuma bai wa mata shawarar neman taimaka daga mutanen da ke kusa da su.

“Ku san ‘yan sanda da lambobin da ya kamata ku kira. Ku bayyana wa makwabtanku, ku gaya masu alamomin da ya kamata su duba don su taimaka maku. Ku bas u lambobinku ‘yan uwanku da za su iya su cece ku.”

Ga wadanda ba za su iya tserewa ba, Esther ta bas u shawara ta karshe. “Kada ku yi shiru don kawai wani ya ji dadi, amma a irin wannan yanayin idan suka fadi wani abu don su tunzura ku, ku yi watsi da su. Idan suka takale ku, dauki littafi ku karanta ko wani abu da zai dauke maku hankali daga kansu.

“Idan za ku iya jure watanni biyu zuwa uku masu zuwa har wannan zaman gidan yak are, ku yi hakan. Bana jin za mu iya kiran wannan matakin magance matsalar, kawai dai a lallaba. A halin yanzu so muke mu tsira da ranmu, don haka ku fadi abin da suke so su ji, ku yi masu abinda suke so ku yi. Kawai ku yi haka don ku tsira da ranku.”

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...