Yadda Koriya ta Kudu ke shirin rage shekarun haihuwa na al’ummarta

“Shekarunka nawa?” Wannan tambaya ce wadda amsarta a bayyane take. Sai dai a Koriya ta Kudu, amsa wannan tambayar na tare da sarkakiya.

A Koriya ta Kudu, ana daukar jariri na da shekara guda a ranar da aka haife shi. Kuma da zarar sabuwar shekara ta iso, sai a kara masa shekara guda. Wannan na nufin jaririn da aka haifa a watan Disamba ya kasance mai shekara biyu da haihuwa ke nan cikin ‘yan makonni.

Sai dai wannan nau’in lissafi na shekara ta Koriya ya kusa sauyawa bayan da zabbben shugaban kasar Yoon Suk-yeol ya kaddamar da wani shiri na soke wannan dadadden tsarin baki dayansa.

Lee Yong-ho shi ne babban jami’in da ke kula da shirin mika masa mulki, kuma ya ce sabuwar gwamnatin za ta duba yadda kasar Koriya ta Kudu za ta koma kan tafarkin lissafin shekarun haihuwa kamar sauran kasashen duniya.

Duk da cewa mutane masu yawa sun rungumi sabon tsarin – amma akwai wasu masana da ke ganin zai yi wuya a iya aiwatar da shirin.

Tambaya É—aya, amsoshi uku

Akwai hanyoyi uku na kidayar shekarun dan Adam a Koriya.

A hukumance, kasar na amfani da tsarin kidaya kamar sauran kasashen duniya, wanda ke amfani da ranar haihuwar mutum domin lissafta shekarunsa na haihuwa.

Amma kasar na da wani tsarin da hukumomi ke amfani da shi, wanda ke cewa dukkan jariran da aka haifa ba su kwana ko daya ba a duniya, amma sukan kara shekara guda a kowace ranar daya ga wata Janairu.

A karkashin wannan tsarin, jaririyar da aka haifa a watan Disambar 2020 za ta kasance mai shekara biyu da haihuwa ke nan a watan Janairun 2022, duk da cewa sai watan Disambar shekarar zai cika shekara biyu da haihuwa.

Sannan akwai tsarin “Shekarar Koriya”, wanda yawancin ‘yan kasar ke amfani da shi. A karkashin wannan tsarin dukkan jaririn da aka haifa na da shekara guda a ranar haihuwarsa, kuma da sabuwar shekara ta zagayo, sai a kara masa shekara guda.

A karkashin wannan tsarin a misali, shahararren mawakin kungiyar nan ta BTS mai kida da wakokin K-pop mai suna Kim Tae-hyung wanda kuma ake kira V, an haife shi ne a ranar 30 ga watan Disambar 1995, wanda a shekarar Koriya yana da shekara 28 da haihuwa, amma shekarunsa a sauran kasashen duniya 27, kuma yana da shekara 27 ke nan idan aka bi daya tsarin na lissafin shekarun ‘yan Koriya.

Ga wasu mutane, shekarar haihuwa ba wani abin damuwa ne ba, amma a Koriya ta Kudu, shekarun mutum na haihuwa abu ne mai muhimmanci.

Wani malamin jami’ar Koriya ya shaida cewa “Ga ‘yan Koriya ta Kudu, gano ko shekarun wani mutumin da suke mu’amula da shi sun zarce nasu ko kaninsu ne ya fi muhimmanci da sanin sunansa saboda al’adar kasar.

“Ta sanin haka ne mutum zai iya sanin yadda zai yi masa magana, da ma irin girmamawar da ta dace da shi.”

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Shekarun Kim Tae-hyung na sauyawa ga wanda ka tambaya

Wannan al’adar ta auna shekaru ta samo asali ne daga China da wasu yankunan Asiya. Sai dai Koriya ta Kudu ce kawai kasar da ta ci gaba da amfani da shi har wannan lokacin da muke ciki.

A misali, wasu iyayen na kokarin sauya shekarun haihuwar ‘ya’yansu saboda sun san za a kara wa jariran da aka haifa a watan Disamba shekara guda.

Wannan kan zama matsala ga yaran nasu a makaranta kuma zai bayyana daga baya yayin da suka girma.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Tun yana takara Yoon Seok-yeol yayi alkawarin soke wannan al’adar ta kidayar shekarun haihuwa na Koriya

Anya ya yi daidai a yi watsi da wannan al’adar kuwa?

Ba wannan ne karon farko da jami’an gwamnatin Koriya ta Kudu ke kokarin sauya al’adar ba domin mayar da kasar daidai da sauran kasashen duniya.

A shekarun 2019 da 2021, wasu ‘yan majalisar kasar sun gabatar da wasu kudurorin doka a gaban majalisar kasar, amma daga baya kokarin nasu bai yi naara ba.

Sai dai masana sun rarrabu kan aiwatar da wannan sabon tsarin kan al’umomin Koriya, duk da cewa sun amince da muhimmancin matakin.

Kuma ko da a hukumance an aiwatar da sabon tsarin, babu tabbaci cewa ‘yan kasar za su rungumi shi – har ma su daina amfani da shekarunsu na al’ada na “Shekarun Koriya”.

More News

Tsoffin gwamnoni sun wawashe sama da naira tiriliyan 2 tun komawa dimokuraÉ—iyya

Aƙalla tsoffin gwamnoni 58 ne ake zargin sun wawure kuma sun yi almubazzarancin jimillar naira Tiriliyan 2.187 a cikin shekaru 25 tun komawa mulkin...

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar Æ´an sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...

Ƴansanda sun kama wanda ya kitsa harin da aka kai wa jirgin ƙasa a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis, ta sanar da kame wanda ake zargin ya shirya harin da aka kai a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna...