Yadda faduwar jam’iyyar Musulunci ta shafi masarautar Morocco—BBC Hausa

  • Daga Magdi Abdelhadi
  • North Africa analyst
King Mohammed VI

Asalin hoton, AFP

Jam’iyyar siyasa mai kishin Islama a Moroko wadda ke shugabantar kasar ta sha kashi a zaɓukan da aka yi a kasar a kwanan nan – wani sakamako da ya janyo ce-ce-ku-ce a yankin Arewacin Afrika.

Jam’iyyar Development and Justice Party (PJD) wadda ita ce jam’iyya mai kishin Islama da ta fara cin zabe a yankin da ma yankin Gabas ta Tsakiya, kujerun da ta yi nasara a baya sun ragu daga 125 zuwa 12 a yanzu.

A 2011 sabuwar Moroko da ‘yan ƙasar da dama ke fatan gani ta fara tabbata.

Lokacin da jam’iyyar PJD ta karɓu a ko ina.

Wata zanga-zanga da ta ɓarke a Tunisia, wadda daga baya aka yi mata take da juyin juya halin kasashen Larabawa ta mamaye ko ina. Inda ta yi gaba da wasu manyan shugabanninn Larabawa kamar su Zine al-Abidine Ben Ali na Tunisia da Hosni Mubarak na Masar, da kuma Muammar Gaddafi na Libya.

Jam’iyyun masu kishin Islama sun ci zaɓuka a Masar da Tunisia, sabon tarihin da mutane ke fatan gani.

Sarkin Moroko Mohammed na biyar ya ga yadda guguwar ta yi watsi da wadannan manyan mutane kuma shi ma za ta iya zama barazana ga sarautarsa.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,
Yayin guguwar juyin juya hali, masu zanga-zanga na neman sauyi inda suke neman a sake fasalin gwamnati

Ya kori duka muƙarrabansa ya kuma rusa majalisar dokokin kasar. Domin rage karsashin zanga-zangar ya sanar da shirin sauya kundin tsarin mulkin kasar domin ƙirƙirar wa Moroko sabuwar hanyar rayuwa.

Daga baya kusan kashi 98.5 cikin dari na kuri’un da aka kaɗa sun amince da aka kaɗa, an yabe shi a matsayin wanda ya kawo sauyi, ya kuma yi yunkurin kawo sauyi a tsarin mulkin kama-karyar sarautar kasar ta hanyar raba iko da wasu mutane a masarautar.

An yi watsin alƙawarin sauyin da sarkin ya yi tare da bayyana su a matsayin na burga a wata zanga-zangar guguwar sauyi da aka yi a watan Fabirairu, karkashin wata inuwa da aka rika yin zanga-zangar juyin juya halin kasashen Larabawa.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,
Jam’iyyar PJD ta kafa wani tarihi na cin zabukan kasar a watan Nuwambar 2011

Abin ya zama har kan titinu domin bukatar kawo sauyi a tsarin masarautar Moroko a sanya a kundin tsarin mulki, ta yadda sarki zai zama “mai rike da ofis ba mai yanke hukunci ba”, ya zama kuma wata alama ta kasa – ta yadda zai zama layi daya da tsarin masarautar Burtaniya ko Scandinavia.

A takaice a kasar, sarki ne ke rike da kusan duka ikon kasar a baya, da kuma sabon kundin tsarin mulki. Shi yake tafiyar da tsare-tsaren harkokin waje da na tsaro da kuma sauransu.

Ya na kuma rike matsayin shugaban addinin na ƙasar – a hukumance kuma shi ne mai tafiyar da harkokin addini, wani tsari da ba a yin amfani da shi a ko ina a duniya a yau, ga kuma ikirarunsu na cewa daular na koma wa ga ta Annabi Muhammad SAW.

Haka kuma, sabon kundin tsarin mulkin kasar ya yi alkawarin kawo sauyi a wasu bangarorin siyasar ƙasar ciki har da jam’iyyar PJD.

Kofin zinare dauke da guba

Duk da cewa kowa ya yi tsammanin kungiyar ta yi karin haske kan kuri’un da aka kada a makon jiya – amma babu wanda ya yi tsammanin za ta sha kashi haka – kazalika shugaban jam’iyyar da mataimakinsa suk fadi, abin da ya janyo suka yi murabus kenan.

Amma za a iya cewa ya yi wuri a bayyana dalilan da suka janyo wannan faduwa. Amma masu sanya idanu sun ce jam’iyyar ta fadi ne sakamakon gaza cika alkawuran da ta dauka.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,
Malamai a kasar na kallon wannan sauyi a matsayin kokarin ruguje ilimi a kasar

Jam’iyyar da ke da sunan “adalci” da kuma “ci gaba” a sunanta ta gaza yin katabus.

A misali, ta yi alkawarin fitar da ‘yan Moroko masu yawa daga talauci, da habbaka ilimi da bangaren lafiya amma ta kasa yin ko daya daga ciki. Maimakon haka sai wagegen gibi da mulkinta ya kara haifarwa tsakanin talakawa da masu kudi.

Wata tambaya guda shi ne yadda aka sanya yaren Faransa a tsarin ilimin kasar- wani babban batu da ake kaffa-kaffar tattaunawa a kansa a kasar da Faransa ta yi wa mulkin mallaka – ta kuma gaza kare dokar da sa ake koyar da kimiyya da yaren Faransa a makarantun kasar.

Masu sharhi sun yi amannar cewa babban kuskuren da jam’iyyar ta yi shi ne jin tana da damar tafiyar da gwamnati yayin da ba ta da cikakken iko, bayan hakan duka na hannun sarki.

A duka fadin yankin, labarin gazawar jam’iyyar ya baza ko ina.

A Masar da sauran kasashen yankin Gulf ana yi wa jam’iyyar kallon wani nau’i na kungiyar ‘yan uwa Musulmi ta Brotherhood, wata jam’iyyar siyasa da aka ayyana a matsayin ta ” ‘yan ta’adda” a wasu kasashe.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,
hamshakin attajiri Aziz Akhannouch zai zama sabon firamoinistan Moroko

Masu sharhi na ganin cewa wannan faduwar da jam’iyyar PJD ta yi kamar an sanya jam’iyyar musuluncin ne a akwatun gawa an rufe.

Mutumin da sarki ya bayar da sunansa a matsayin wanda zai kafa sabuwar gwamnati, Aziz Akhannouch, wanda wani biloniya ne da ke jagoyantar jam’iyyar National Rally of Independents (RNI), wanda ya lashe zabe da adadi mafi yawa, ya ce “gwamnati za ta yi kokarin aiki da sabbin hanyoyin da aka tsara domin tafiyar da masarauta”.

Da yake sharhi kan lamarin tsohon dan jaridar Moroko Hamid Elmahdaouy, ya rubuta cewa duka Firaiministocin kasar da suka gabata magana daya suka fada da na yanzu.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon ɗaya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...