Yadda Boko Haram ta tilasta wa mutane tserewa daga Geidam

Mutanen Geidam

Asalin hoton, Getty Images

Bayanai sun tabbatar da cewa mazauna Geidam da ke jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya na ci gaba da tserewa daga garin sakamakon tashin hankalin da ake fama da shi a yankin.

Mazauna garin na Geidam wadanda BBC Hausa ta yi magana da su sun ce daruruwan mutane ne suke ci gaba da ficewa daga garin zuwa makwabtan garuruwa wasunsu ma a kafa domin kauce hare-haren mayakan kungiyar Boko Haram.

Wani mutum da ya je kwaso kayansa a cikin garin domin ya tsere ya shaida mana cewa “an fara harbe-harbe ina cikin gida ina diban kayana. Abin da na debo kawai na fito na yi maza na bar garin. Su ‘yan Boko Haram da sojoji suna gabas da gari suna ta harbe-harbe.”

Ya kara da cewa mayakan na Boko Haram suna wata kasuwa kodayake mutane suna iya shiga garin su debi kayansu domin su fice daga Geidam.

A cewarsa mayakan na Boko Haram sun yanka wani malamin firamare da kuma wani yaro lamarin da ya sa mutanen garin ke ci gaba da yin tururuwa suna tsere wa daga garin.

Asalin hoton, HQNIGERIANARMY

A nata bagaren, wata mata da ta tsere daga garin na Geidam, ta ce an jefa malamin atilari a gidansu lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum 11 ciki har da ‘yar uwarta mai shayarwa.

“Sai [matar] ta shiga daki suka zauna da ‘ya’yan surukarta su biyar da budurwa har an kai mata sadaki. Wannan jefa atilarin aka ce da aka yi na farkon nan wallahi ba a sani ba, Allah shi ya bar wa kansa sani kawai aka ji karar abu. Sai surukar ta fito tana salati daki ya kama da wuta,” in ji ta.

Ta kara da cewa yanzu ita ce ta ke shayar da É—iyar ‘yar uwarta da harin na atilari ya kashe.

Matar ta ce yanzu sun fice daga garin na Geidam tana mai cewa “mun fito a kafa mu da ‘ya’ya muna kuka kamar dabbobi.”

Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ya ce suna cikin tsaka mai-wuya sakamakon hare-haren mayakan Boko Haram da suka tayar musu hankali tun ranar Juma’ar makon jiya.

Mai Mala ya ce sanin kowa ne halin da ake ciki a yankunan arewa maso gabashin Najeriya, sai dai hare-haren da suke gani a yanzu na tada hankula matuka kuma ya zama dole a tunkare su.

A tattaunawarsa da BBC, gwamna ya ce a baya komai ya yi sauki amma a wannan lokaci abin ya tsananta, saboda ba a san dalilan mayakan ba, kuma zuwansu na wannan lokaci ya sha bamban da wanda aka saba gani a baya.

A nata bangaren, rundunar sojin kasar ta ce ta kashe mayakan Boko Haram 21 a garin na Geidam.

Kakakin rundunar Birgediya Janar Mohammed Yerima ya ce suna fuskantar kalubale wajen fitar da ‘yan Boko Haram daga garin saboda sun saje cikin jama’a.

(BBC Hausa)

More News

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...

ÆŠan agajin Izala ya samu lambar yabo, kujerar hajji, kyautar mota bayan ya tsinci naira miliyan 100 ya mayar wa mai su

Salihu AbdulHadi Kankia, mamba ne na kungiyar agaji ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), ya samu yabo da tukuicin mayar da...