Shugaban Amurka Joe Biden, ya yi kira ga kasashen Majalisar Dinkin Duniya da su tashi tsaye don yakar abin da ya kira laifukan yaki daga Rasha.
A cewarsa, tabbatar da ‘yancin cin gashin kan kowace kasa da kuma kare hakkin bil’adama shi ne babban abin da ke cikin daftarin Majalisar Dinkin Duniya.
Joe Biden na magana ne a wani bangare na taron Majalisar Dinkin Duniya na shekara-shekara a birnin New York.
A shekara ta biyu a jere ya ce wannan taro ya yi duhu da inuwar wannan yaki da Rasha ta haifar ba tare da tsayawa ba.
“Rasha ta yi imanin cewa duniya za ta nuna gajiyawa, kuma duniya za ta bar Rasha ta zalunci Ukraine, ba tare da jin kai ba.