Ana ganin rikicin da ake yi a kasar Sudan zai zo karshe yayin da bangarorin da suke fada suka hallara a kasar Saudiyya domin gudanar da tattaunawar zaman lafiya a karon farko tun bayan barkewar yakin a tsakiyar watan Afrilu.
Za a yi tattaunawar ne bayan Saudiyya da Amurka sun dauki nauyinta.
Yarjejeniyar tsagaita bude wuta da dama a baya sun ci tura tun farkon yakin makonnin da suka gabata.
In ba a manta dai wannan yaƙi ya shafi mutane da yawa, ciki har da ƴan Najeriya da ke karatu a ƙasar ta Sudan.
Hakan ya tilasta wa gwamnatin Najeriya kwaso ɗaukacin ƴan kasar da ke can bayan an samu matsaloli da dama a wannan yunkurin.