Yaƙin Sudan: Mutane sama da 7,000, ciki har da ƴan Najeriya, sun tsangare a Misra

Gwamnatin tarayya a ranar Juma’a ta yi kira ga hukumomin da abin ya shafa a kan iyakokin kasar Sudan da su samar da yanayin jin dadin jama’a ga ‘yan kasar kimanin 7,000 ciki har da ‘yan Najeriya, su samu damar shiga wurare daban-daban ba tare da wata matsala ba.

Shugabar hukumar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa, wacce ta yi wannan kiran, ta ce ba a ba ‘yan kasar damar tsallakawa kasar Masar ba tun zuwansu da yammacin ranar Alhamis.

Dabiri-Erewa, a ranar Alhamis, ta tabbatar da isowar rukunin farko na ‘yan Najeriya da suka makale a Sudan a kan iyakar Aswan a Masar.

Dabiri-Erewa, wadda ta tabbatar da faruwar lamarin a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce tuni aka rufe kan iyakar lokacin da daliban suka isa wurin.

Sai dai a wata sanarwa mai dauke da sa hannun Gabriel Odu, Sashen Watsa Labarai na NiDCOM, ya ce “Tawagar Najeriya a Masar ta yi aiki tukuru a kan hakan yayin da mahukuntan Masar ke nanata bayar da biza ta ‘yan kasashen Afirka don komawa kasashensu.

“Ta yi kira ga hukumomin Masar da su ba wa matafiya da suka kaɗu damar wucewa zuwa kasashensu daban-daban na Afirka.”

More from this stream

Recomended