Wike Ya Ziyarci Ganduje

Tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya ziyarci shugaban jam’iyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje a Abuja ranar Talata.

Wike na ɗaya daga cikin mutanen da aka tantance a majalisar dattawa da za a naɗa a matsayin ministoci.

A yan kwanakin nan ana ta rade-radin cewa tsohon gwamnan zai sauya sheka ya zuwa jam’iyar APC.

A zaɓen da aka gudanar Wike ya nuna adawarsa ga ɗan takarar jam’iyars ta PDP, Alhaji Atiku Abubakar duk da cewa ya musalta zargin da ake masa na yiwa jam’iyarsa zagon ƙasa.

More from this stream

Recomended