Watakila Juanma Lillo ya zama mataimakin Guardiola

Juanma Lillo

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Watakila Juanma Lillo ya kama aikin mataimakin Guardiola a Manchester United, bayan da ya bar aikin horar da Qingdao Huanghai ta China.

Dan kasar Spaniya ya yi nasarar kai Qindao babbar gasar China a kakar bara, amma yanzu wasu rahotanni na cewar zai yi aikin mataimakin koci a gasar Premier League.

Kamar yadda Daily Mail da Daily Mirror suka wallafa kocin yana da kwarewar da zai daga martabar Manchester City a wasannin kwallon kafa.

Guardiola bai da mataimaki tun bayan da Mikel Arteta ya karbi aikin jan ragamar Arsenal a cikin watan Disamba.

Wasu da aka sa ran za su maye gurbin Arteta a Etihad sun hada da Xabi Alonso da Vincent Kompany da sauran fitattun masu horar da tamaula.

Lillo ya tabbatar da barin kungiyar ta China wadda ya bai wa dalilin cewar zai je ya kula da mahaifiyarsa wadda ke fama da jinya.

Guardiola ya taka kwallo a karkashin Lillo a kungiyar Dorados ta Mexico daga nan ya yi ritaya daga taka-leda.

Lillo ya horar da Tolosa CF da Mirandes da Cultural Leonesa da UD Salamanca da Real Oviedo da Tenerife da Real Zaragoza da Ciudad Murcia.

Sauran kungiyoyin da ya ja ragama sun hada da Terrassa da Dorados da Real Sociedad da Almeria da Millonarios da Atletico Nacional da kuma Vissel Kobe.

Ya kuma yi aikin mataimaki a tawagar kwallon kafar Chile da kuma Sevilla mai buga gasar La Liga ta Spaniya.

Ranar 17 ga watan Juni za a ci gaba da gasar Premier, inda Manchester City za ta buga kwanatan wasa da Arsenal.

A kuma ranar za a kece raini tsakanin Aston Villa da Sheffield United.

Manchester City tana mataki na biyu a teburin Premier da tazarar maki 25 tsakaninta da Liverpool ta daya tun bayan da aka dakatar da wasanni a cikin watan Maruis saboda bullar cutar korona.

More News

Ribadu ya koka kan yadda jami’an tsaro suke sayarwa da Æ´an ta’adda bindigogi

Mai bawa shugaban shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu ya ce wasu daga jami'an Æ´an sanda da kuma sojoji suna É—aukar bindigogi daga...

Gwamnan Legas Sanwo-Olu ya kara mafi ƙarancin albashi zuwa naira 85,000

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana shirin gwamnatinsa na fara biyan sabon mafi karancin albashi na N85,000 ga ma'aikatan jihar.Sanwo-Olu ya bayyana hakan...

Sama da mutane 100 aka tabbatar sun mutu a gobarar hatsarin tankar mai a Jigawa

Rundunar Æ´an sandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutane 140 a hatsarin gobarar tankar mai da ta faru a garin Majia dake kan...

Sojoji sun kashe É—an Boko Haram a Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya na Birged Ta 21 dake aiki da rundunar Operationa HaÉ—in Kai dake aikin samar da tsaro a yankin arewa maso...